Buhari ya kalubalanci gwamnoni kan inganta ci gaban gine-gine

Buhari ya kalubalanci gwamnoni kan inganta ci gaban gine-gine

A yayin da a yau Juma'a, 14 ga watan Dasumba na 2018, shugaban kasa Muhammadu Buhari, yayin ganawarsa da gwamnoni na jihohi 36 da ke fadin kasar nan a fadar Villa dake birnin Abuja, ya yi wani muhimmin kira domin inganta ci gaban kasa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kirayi gwamnoni na jihohi 36 dake fadin kasar nan kan sake zage dantsen su wajen inganta ci gaba na gine-gine cikin jihohin su domin habakar tattalin arziki na kasa baki daya.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da gwamnonin a yau Juma'a cikin fadarsa ta Villa dake babban birnin kasar nan na tarayya.

Manema labarai sun ruwaito wannan rahoto ne daga bakin shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara, bayan ganawar sirrance da ta gudana tsakanin gwamnonin da kuma shugaban kasa Buhari.

Buhari ya kalubalanci gwamnoni kan inganta ci gaban gine-gine

Buhari ya kalubalanci gwamnoni kan inganta ci gaban gine-gine
Source: Depositphotos

Gwamna Yari yake cewa, kamar kullum, shugaban kasa Buhari ya sake tunatar da su dangane da barazana ta durkusa da ke ci gaba da tunkarar tattalin azrikin kasa, inda ya yi kira a garesu kan jajircewa da kuma kwazo bisa aiki wajen inganta ci gaban kasar nan ta hanyoyi da dama da za su fidda ita zuwa ga tudun tsira.

KARANTA KUMA: Buhari ya gargadi 'Yan Najeriya kan fahimtar juna da zaman lafiya yayin zaben 2019

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, ummul aba isin wannan ganawa ta biyo bayan zaman tattaunawa gami da tuntube-tuntube na shawarwari kan mafi karancin albashin ma'aikatan kasar nan.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, ganawar gwamnonin tare da shugaban kasa Buhari ta gudana ne bayan sun halarci zaman majalisar zantarwa kan tattalin arziki da ya gudana cikin fadar bisa jagorancin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel