Yanzu Yanzu: Aisha Buhari ta isa Uyo don kaddamar da aikinta (hotuna)

Yanzu Yanzu: Aisha Buhari ta isa Uyo don kaddamar da aikinta (hotuna)

- Uwargidan Shugaban Kasa Muhammadu Buhar, Hajiya Aisha ta isa Uyo, babbar birni jihar Akwa Ibom

- Ta kai ziyara jihar ne domin kaddamar da wata gidauniyarta na tallafawa mata da yara a jihar

Uwargidan Shugaban Kasa Muhammadu Buhar, Hajiya Aisha ta isa Uyo, babbar birni jihar Akwa Ibom domin kaddamar da aikinta na shirin tallafawa matan jihar.

Aisha Buhari ta isa filin kamfen din na nsimaekere da ke Uyo a yau Juma’a, 14 ga watan Disamba domin kaddamar da shirin.

Wannan gidauniya dai da uwargidan shugaban kasar za ta kaddamar kungiya ce mai zaman kanta don ci gaban mata da yara wato Future Assured.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shekarau, Yerima, Yayale na a fadar shugaban kasa don ganawa da Buhari

A wani lamari na daban, mun ji cewa ta kalubalanci 'yan Najeriya a kan su tashi tsaye domin yakar wasu mutane biyu da suka hana ruwa gudu a gwamnatin mijinta.

Uwargidan shugaban kasar na wadannan kalamai ne yayin halartar wani taron mata masu goyon bayan Buhari da Osinbajo su maimaita mulki.

Duk da bata ambaci sunayen mutane biyu ba, ta bayyana cewar sun kankane komai a gwamnatin da mutum miliyan 15 suka zaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT Hausa

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel