An sako Fashola a gaba kan kalami a kan matsalar wutar lantarki a Najeriya

An sako Fashola a gaba kan kalami a kan matsalar wutar lantarki a Najeriya

Al'ummar Najeriya sunyi ca a kan ministan makamashi, ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola bayan ya ce gwamnatin tarayya ba ta da laifi a kan matsalar wutan lantarki a Najeriya.

Ministan ya ce 'yan kasuwa da ke aiki a fannin samar da wutan lantarkin ne ke da laifi.

Fashola ya yi wannan furucin ne a daren Laraba a Abuja yayin tattaunawar da Nextier Power ta shirya.

Ministan ya ce tunda an sayar wa 'yan kasuwa fanin samar da wutan lantarkin, gwamnati ba ta da wani laifi idan 'yan Najeriya ba su samun wadatacen wutar lantarki.

An sako Fashola a gaba kan kalami a kan matsalar wutar lantarki a Najeriya

An sako Fashola a gaba kan kalami a kan matsalar wutar lantarki a Najeriya
Source: Depositphotos

"Tabbas akwai matsaloli kuma za mu warwaresu.

"Amma ina son in tunatar da ku cewa gwamnatin da ta shude ta sayar da dukkan kayayakin hukumar makamashi kafin in zo, saboda haka idan ba ku da wutar lantarki, ba matsalar gwamnati bane. Ya kamata mu fadawa kan mu gaskiya," kamar yadda Punch ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Sojoji sun ragargaji 'yan ta'addar Zamfara, hotunan wadanda suka mutu

Ministan ya ce a sauran bangarorin gwamnati, Idan akwai matsala my ramen da ke kula da fannin ake yiwa korafi ba gwamnati ba.

"Aiki na sanya idanu ne da kuma tsara dokoki, na ga matsala kuma ba zan kawar da kai ba, shiyasa na shigo a dama da ni. Masu bukatar transiforma su dena zuwa wuri na domin ba ma'aikata na ke samar da transiforma ba a yanzu."

Sai dai wannan furucin da ministan ya yi bai yiwa wasu 'yan Najeriya dadi ba, kuma da dama sun mayar da martani da kakausan murya.

Lanre Suraj, shugaban HEDA, ya shaidawa Premium Times cewa giyar mulki ce ke dibar ministan shi yasa ya fara girman kai.

Matt Etta, wani mai amfani da shafin Twitter yace, "Wai Fashola ne ke cewa babu laifin gwamnati a cikin matsalar wutan lantarki saboda gwamnatin da ta shude ta sayarwa 'yan kasuwa. Shin ba aikin ministan makamashi bane ya tabbatar suna abinda ya dace? Mene yasa aka nada shi Ministan makamashi?."

Wani Olamide Ogunduyile ya rubuta: "Wannan abin kunya ne Fashola ya yi. Akwai miliyoyin 'yan Najeriya da ba su da wuta amma ka dora laifin a kansu. Ya kamata ka gyra."

Wani mai sharhi a kan al'amurran yau da kullum, Farooq Kperogi ya soki ministan a shafinsa na Twitter.

Ya rubuta: "A ranar 12 ga watan Yulin 2014, Fashola ya ce korar PDP daga mulki ne kawai zai sanya 'yan Najeriya su samu wutar lantarki. An kori PDP a 2015 kuma ya zama ministan Makamashi amma bayan shekaru 4 ya ce rashin wuta ba laifin gwamnati ba ne,' wannan shine yaudara."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel