Majalisar UN ta ja-kunnen Kasashe game da rikicin Boko Haram

Majalisar UN ta ja-kunnen Kasashe game da rikicin Boko Haram

Majaliar dinkin Duniya ta yi kira ga Kasashen waje su kara a ido kan ‘Yan ta’addan Boko Haram. Wani babban Jami’in UN ne yayi wannan kira na musamman a cikin wannan makon a kasar Amurka.

Majalisar UN ta ja-kunnen Kasashe game da rikicin Boko Haram

An gargadi Kasashen Afrika game da rikicin Boko Haram
Source: UGC

Wakilin Afrika ta tsakiya a babban ofishin Majalisar dinkin Duniya na Nahiyar watau Francoise Fall ya gargadi manyan Kasashen Duniya su zura idanu da kyau kan ‘Yan ta’addan Boko Haram da ke ta’adi a Yankin tafkin Chadi.

Mista Fall yayi wannan gargadi ne a gaban Majalisar tsaro na Hedikwatar Majalisar dinkin Duniya da ke Birnin New York a Kasar Amurka inda yace ‘Yan ta’addan na iya kai munanan hari kan Jami’an tsaro da kuma sauran Jama’a.

KU KARANTA: Sojoji sun ragargaji 'yan ta'addar Zamfara har Lahira

Kamar yadda mu ka samu labari daga Hukumar dillacin Najeriya, Fall yayi wa kwamitin tsaro na UN wannan jawabi ne a wajen wani taro, yana mai kira ayi kokarin duba silar rikicin da ya addabi Arewa maso Gabashin Najeriya.

Fall ya kuma nemi a kara kaimi wajen tsare kan iyakoki inda ya bayyana cewa rikicin zai iya aukawa sauran Kasashen Nahiyar ya mamaye su. Fall duk yayi wannan jawabi ne a gaban Majalisar tsaron UN mai dauke da mutane 13.

Kwanaki wani tsohon babban Jami’in ‘Yan Sanda a Kasar Birtaniya yayi fashin baki game da sha’anin tsaro a Arewacin Najeriya inda yace akwai babbar matsala a tsarin shugabanci a gidan Sojin Kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel