Gwamnatin tarayya ta kaddamar da bincike kan Sanata David Mark

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da bincike kan Sanata David Mark

Gwamnatin tarayya ta hanyar kwamitin fadar shugaban kasa ta musamman kan bincike da kwato kudin sata ta kaddamar da bincike kan wasu dukiyoyi a kasashen waje da ake kyautata zaton na tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, ne.

Jaridar Punch ta samu rahoton a ranan Alhamis cewa kwamitin ta fara bincike ne tare da hukumar leken asirin Najeriya NIA.

An tattaro cewa sun fara wannan bincike ne bisa ga rahoton 'Panama Papers' da wata kafar yada labarai ta saki kan David Mark da wasu yan siyasan Najeriya da na duniya masu dukiyoyi a fadin duniya.

KU KARANTA: Shekarau, Yerima, Yayale na a fadar shugaban kasa don ganawa da Buhari

A watan Mayun 2016, kungiyar yan jarida masu bincike da dunya ta saki takarda kunshe da cinikayya da dukiyoyin wasu masu kudi na duniya. A wannan takarda, akwai sunayen yan siyasan Najeriya da dama a ciki.

Wata majiya na kusa da tsohon shugaban majalisar dattijan ta bayyana cewa kwamitin binciken ta gayyaci David Mark kan wasu dukiyoyi 20 da kuma kudin harajin da yaki biya.

An samu labarin cewa an gayyaci Mark ya bayyana gaban kwamitin ranan 11 ga watan Disamba 2018 amma ya mayar da martani cewa ba zai samu damar zuwa ba saboda yanayi na rashin lafiya da yake fama da shi.

Yanzu ya bukaci a daga masa kafa ya bayyana ranan 21 ga watan Disamba, 2018.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel