2019: Yan takarar mataimakin shugaban kasa Osinbajo da Peter Obi za su yi muhawara

2019: Yan takarar mataimakin shugaban kasa Osinbajo da Peter Obi za su yi muhawara

Za a tafka muhawara tsakanin Yemi Osinbajo (APC), Peter Obi (PDP), Umma Getso (YPP), Alhaji Abdulganiyu Galadima (ACPN) da kuma Khadijah Abdullahi-Iya (ANN).

Rahotanni sun kawo cewa masu neman takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyun siyasar kasar za su tafka muhawara a akn zaben 2019 a ranar Juma’a.

Muhawarar, wacce wata kungiya mai suna the Nigerian Election Debate Group (NEDG) da kuma kungiyar Broadcasting Organisations of Nigeria (BON) suka shirya a Abuja, za ta mayar da hankali ne kan irin tanadin da 'yan takarar ke da su wurin inganta rayuwar al’umman kasar.

2019: Yan takarar mataimakin shugaban kasa Osinbajo da Peter Obi za su yi muhawara

2019: Yan takarar mataimakin shugaban kasa Osinbajo da Peter Obi za su yi muhawara
Source: Facebook

Ana sanya ran cewa 'yan takarar mataimakin shugaban kasa biyar za su halarci muhawarar.

Wadannan yan takara sun hada da: Yemi Osinbajo (APC), Peter Obi (PDP), Umma Getso (YPP), Alhaji Abdulganiyu Galadima (ACPN) da kuma Khadijah Abdullahi-Iya (ANN).

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shekarau, Yerima, Yayale na a fadar shugaban kasa don ganawa da Buhari

Shugaban BON, John Momoh, ya ce za a watsa muhawarar kai-tsaye a dukkan tasoshin BON (NTA, Channels TV, AIT, Silverbird TV, da sauran su).

Ya kara da cewa za a iya kallon muhawarar kai-tsaye a Facebook da YouTube da kuma Twitter.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel