'Yan Jarida 251 na ci gaba da shan dauri a gidajen kaso dake fadin Duniya - CPJ

'Yan Jarida 251 na ci gaba da shan dauri a gidajen kaso dake fadin Duniya - CPJ

Kwamitin bayar da kariya tare da tsare mutuncin 'yan jarida, Committee to Protect Journalists, CPJ, ya bayyana adadin 'yan jarida dake garkame a gidajen kaso a fadin duniya a halin yanzu bisa laifuka na nuna ƙiyayya da kuma adawa.

Cikin shekaru uku da suka gabata kawowa yanzu, akwai kimanin 'yan jarida 251 da ke garkame a gidajen kaso a fadin duniya kamar yadda binciken kwamitin na CPJ ya bayyana.

Kwamitin ya bayyana cewa, hukumomi ma su rike da tsare-tsaren mulki ke da alhakin amfani da gidajen kaso wajen kunshe bakunan 'yan jarida ma su watsa rahotanni na nuna ƙiyayya da kuma adawa a gare su.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, binciken kwamitin na CPJ ya tabbatar da cewa, akwai adadin 'yan jarida 251 da ke ci gaba da shan dauri a gidajen kaso da ke fadin duniya sakamakon laifukan da suka aikata a bakin aikin su.

'Yan Jarida 251 na garkame a gidajen kaso dake fadin Duniya - CPJ

'Yan Jarida 251 na garkame a gidajen kaso dake fadin Duniya - CPJ
Source: Getty Images

Binciken ya tabbatar da cewa, kasar Masar, China, da kuma Saudiyya ke kan gaba wajen garkame 'yan jaridu musamman a shekarar da ta gabace mu.

Kazalika binciken ya tabbatar da cewa, kasar Taki ita ce kasar da ta yiwa sauran kasashen duniya fintikau ta fuskar daure 'yan jarida da halin yanzu adadin su ya kai kimanin 68 cikin shekaru uku da suka gabata.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, binciken CPJ ya tabbatar da cewa mafi akasarin 'yan jaridun na bai wa diga-digan su hutu ne a gidajen kaso sakamakon laifukan su na wata rahotanni na shaci fadi da marasa tushe.

Shugaban kwamitin CPJ, Joel Simon, shine ya bayyana hakan yayin ganawar sa da manema labarai, inda ya bayyana takaicin sa kwarai da aniyya dangane da wannan lamari da ya misalta a matsayin cin zaradi ga 'yan jarida.

KARANTA KUMA: Albashin Ma'aikata: Gwamnonin Najeriya na ganawa da Shugaban Kasa Buhari

A wani rahoton mai nasaba da wannan, cikin adadin 'yan jaridu 251 da ke shan dauri a fadin duniya, akwai kimanin 33 da suka kasance Mata, kuma hudu daga cikin su sun fito ne daga kasar Saudiyya sakamakon rubuce-rubucen da suka wallafa kan hakkin Mata.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a yayin da shirye-shiryen aikin hajji na 2019 ya kan kama, hukumar jin dadin alhazai ta Najeriya ta bayyana cewa, hukumar kula da Alhazai ta kasar Saudiyya ta kayyade adadin Maniyyata 95, 000 da za ta bai wa damar sauke farali a badi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel