Yanzu Yanzu: Shekarau, Yerima, Yayale na a fadar shugaban kasa don ganawa da Buhari

Yanzu Yanzu: Shekarau, Yerima, Yayale na a fadar shugaban kasa don ganawa da Buhari

Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmed Yerima, da tsohon babban sakataren gwamnatin tarayya, Yayale Ahmed sun jagoranci wata tawagar yan siyasa zuwa fadar shugaban kasa domin ganawa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Wasu tsoffin gwamnoni uku sun jagoranci wata tawagar kungiyar siyasa zuwa ganin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a fadarsa a yau Juma'a, 14 ga watan Disamba.

Kungiyar sun ziyarci shugaba Buhari ne a karkashin inuwar “National Network for Community and Youth Development.”

Shekarau ya kasance makusancin shugaba Buhari kafin su raba jiha a lokacin zaben shugabancin kasa na 2011.

Sabanin da aka samu tsakanin shugabannin biyu wadanda a lokacin suke jam’iyyar ANPP ya sanya Buhari kafa jam’iyyar CPC, yayinda Shekarau ya ci gaba da kasance a ANPP sannan ya yi takara da shugaba Buhari a 2011.

Yanzu Yanzu: Shekarau, Yerima, Yayale na a fadar shugaban kasa don ganawa da Buhari

Yanzu Yanzu: Shekarau, Yerima, Yayale na a fadar shugaban kasa don ganawa da Buhari
Source: UGC

Bayan haka suka sake haduwa a jam’iyyar All Progressives Congress (AP) bayan tsoffin jam’iyyunsu sun kafa wata sabuwar jam’iyya.

Sai dai kuma tsohon gwamnan ya sake barin APC zuwa PDP sakamakon banbancin dake tsakaninsa da Rabiu Kwankwaso.

KU KARANTA KUMA: Dokar zabe: APC ta zargi PDP da yan Rasha da yunkurin sauya sakamakon zabe a kwamfutar INEC

Haka zalika a lokacin da Kwankwaso ya koma PDP sais hi kuma Shekarau ya bar PDP zuwa APC inda a yanzu suke jam’iyya guda da Buhari.

Wannan shine karo na farko da Shekarau zai gana da Buhari tun bayan dawowarsa jam’iyya mai mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel