Sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ba dole bane - Dan takarar shugaban kasa

Sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ba dole bane - Dan takarar shugaban kasa

- Dan takarar shugaban kasa na SDP, Donald Duke ya ce babu bukatar sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

- Tsohon gwamnan na Cross Rivers ya ce kundin tsarin mulki ya tanadar da hukunci ga duk wanda ya saba dokokin zabe

- Dan takarar shugaban kasar ya kuma bukaci hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta dage wajen fadakar da masu kada kuri'a

Dan takarar shugabancin kasar na jam'iyyar Social Democratic Party, Donald Duke ya ce ba bu bukatar 'yan takara su sanya hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya da aka bukaci 'yan takarar su rattaba hannu a kai.

Ya ce akwai dokoki a kudin tsarin mulkin Najeriya da za su hukunta dukkan wadanda suka aikata laifi yayin gudanar da zaben.

Sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ba dole bane - Dan takarar shugaban kasa

Sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ba dole bane - Dan takarar shugaban kasa
Source: Depositphotos

Duke, wanda tsohon gwamna ne na jihar Cross River ya yi wannan jawabin ne a wajen taron kaddamar da wani littafi mai suna "The coming revolution: A manifestor for national greatness," wanda Farfesa Iyorwuese Hagher ya rubuta.

DUBA WANNAN: Boko Haram ta kara yaduwa a Najeriya - Abdulsalami Abubakar

Ya ce, "Babu bukatar a rattaba hannu a kan wani yarjejeniyar zaman lafiya saboda akwai dokoki.

"Kawai dai muna son mu nuna cewa za muyi takara ne.

"Akwai dokokin da za su hukunta wadanda ba su son biyaya ga dokokin kasa. Haka ya kamata ya kasance a tsakanin al'umma da ke rayuwa cikin tsari."

Sai dai duk da hakan, Duke yabawa wadanda suka shirya yarjejeniyar, ya ce za ta taimaka wajen hana shugabanin siyasa tayar da hankullan al'umma a zabe mai zuwa.

"INEC ta gudanar da aikinta na hukunta duk 'yan takarar da aka samu suna sayan kuri'u domin hakan zai sanya 'yan takarar su shiga taitayin su.

"Idan ba a dauki mataki ba, kowa zai rika aikata abinda ya ga dama ne."

Ya kuma yi kira ga INEC ta kara dagewa wajen wayar da kan masu kada kuri'a domin hakan zai taimaka wajen gudanar da zabe cikin zaman lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel