Dokar zabe: APC ta zargi PDP da yan Rasha da yunkurin sauya sakamakon zabe a kwamfutar INEC

Dokar zabe: APC ta zargi PDP da yan Rasha da yunkurin sauya sakamakon zabe a kwamfutar INEC

- Jam’iyyar APC ta zargi babbar jam’iyyar PDP da yunkurin yin amfani da dokar zabe wajen yiwa INEC shigar sauri, ta hanyar shiga kwanfutar ta ba bisa ka’ida ba a lokacin zabe

- Jam’iyyar mai mulki ta zargi jam’iyyar adawa da kokarin amfani da wasu yan Rasha wajen sauya sakamakon zabe a kwamfutar INEC

- Ita ma PDP ta yi ikirarin cewa ta gano wani makirci da hukumar zabe da Buhari ke yi don yin magudin zaben 2019 ta hanyar amfani da wuraren zabe da aka kafa ba bisa ja’ida ba a kasashen Chadi da Nijar

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta zargi babbar jam’iyyar adawar kasar ta Peoples Democratic Party (PDP) da yunkurin yin amfani da dokar zabe wajen yiwa hukumar zabe mai zaman kanta shigar sauri, ta hanyar shiga kwanfutar ta ba bisa ka’ida ba a lokacin zabe.

Kungiyar kamfen din shugabancin kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party itama a jiya ta yi ikirarin cewa ta gano wani makirci da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi don yin magudin zaben 2019 ta hanyar amfani da wuraren zabe da aka kafa ba bisa ja’ida ba a kasashen Chadi da Nijar.

Dokar zabe: APC ta zargi PDP da yan Rasha da yunkurin sauya sakamakon zabe a kwamfutar INEC

Dokar zabe: APC ta zargi PDP da yan Rasha da yunkurin sauya sakamakon zabe a kwamfutar INEC
Source: Depositphotos

Mataimakin sakataren labaran APC, Yekini Nabena a wani hira da manema labarai a Auja yace PDP ta dauko wasu yan kasar Rashawa tare da kudirin cewa su shiga kwamfutar hukumar zabe mai zaman kanta ba bisa ka’ida ba a lokacin zaben watan Fabrairu.

KU KARANTA KUMA: Wajibi ne Najeriya ta taimakawa ECOWAS - Buhari

Nabena ya nuna mamaki kan dalilin da yasa a yanzu hankalin PDP bai kwanta da dokar da aka dade ana amfani da shi wajen gudanar da zaben kasar idan har babu wata a kasa.

A cewar shi, abunda PDP ke yi a yanzu duk shiri ne da ta kulla a lokacin ganawar da tayi a Dubai tare da dan takararta, Atiku Abubakar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel