Wajibi ne Najeriya ta taimakawa ECOWAS - Buhari

Wajibi ne Najeriya ta taimakawa ECOWAS - Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba kungiyar kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) tabbacin cewa kasar Najeriya za ta ci gaba da tallafawa yankunan da ke kungiyar. Ya bayar da tabbacin ne lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga karkashin jagorancin kakakin majalisar ECOWAS, Moustapha Cisse Lo.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba kungiyar kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) tabbacin cewa kasar Najeriya za ta ci gaba da tallafawa yankunan da ke kungiyar.

Ya bayar da tabbacin ne lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga karkashin jagorancin kakakin majalisar ECOWAS, Moustapha Cisse Lo, a ranar Alhamis, 13 ga watan Disama a fadar shugaba kasa da ke Abuja.

Wajibi ne Najeriya ta taimakawa ECOWAS - Buhari

Wajibi ne Najeriya ta taimakawa ECOWAS - Buhari
Source: UGC

“Kasancewa na shugaban kasar Najeriya kuma shugaban kasashen ECOWAS, wajibi ne ga Najeriya ta taimakawa kungiyar,” kamar yadda shugaban kasar ya bayyana a wata sanarwa daga mai bashi shawara a harkar labarai, Femi Adesina.

Furucin shugaan kasar martani ne ga bukatar kakakin kungiyar, wanda suka hada da masauki, biyan alawus, da kuma sauran lamaran day a shafi jin dadinsu.

KU KARANTA KUMA: A baya mun yi soyayya da Adam A. Zango, sai dai yanzu mutunci ne kawai tsakaninmu – Nafisa Abdullahi

Ya kara da cewa, “Zamu kula da lamarin. Hakkinmu ne kula da ku. Zamu duba lamuran da suka gabatar.”

Kakakin majalisar Cisse Lo ya gode ma kasar Najeriya da ta bayar da fili a Abuja ga majalisar ECOWAS domin gina sakatariyarta na din-din-din.

Ya kuma yabama gwamnati mai ci kan jajircewarta a harkar tsaro da yaki da cin hanci da rashawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel