Babban Alkalin Najeriya ya nemi a nada sabbin Alkalai domin harkallar Zaben 2019

Babban Alkalin Najeriya ya nemi a nada sabbin Alkalai domin harkallar Zaben 2019

Mun samu cewa a jiya Alhamis, babban Alkali na Najeriya, Mai Shari'a Walter Onnoghen, ya bayar da umarni na nada sabbin Alkalai domin tunkarar dambarwa da ka iya biyo bayan harkallar babban zaben kasa na 2019.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, babban lauyan ya yi wannan muhimmin kira ne da manufa ta watsa Alkalai cikin hukumomin Shari'a na kasar nan domin tunkarar dambarwa ta korafe-korafe bayan gudanar babban zabe na badi.

Mai Shari'a Onnoghen ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa yayin gabatar da jawabai a taron shekara na Kotun daukaka kara da aka gudanar cikin babban birnin kasar nan na tarayya.

Babban Alkalin Najeriya; Mai Shari'a Walter Onnoghen

Babban Alkalin Najeriya; Mai Shari'a Walter Onnoghen
Source: Facebook

Ya ke cewa, akwai muhimmiyar bukata ta yiwa zaben kasar nan rubdugu a bisa dalili na dambarwa ta korafe-korafe da ka iya biyo bayan zaben 2019 domin tabbatar da sahihanci da kuma inganci na hukumar Shari'a ta kasa.

Kazalika wannan lamari zai inganta nagarta ta Alkalan kasar nan gami da kwarewa bisa aiki da za ta tabbatar da cancantar su ta gogayyar kafadu ko ina a fadin duniya.

KARANTA KUMA: Jam'iyyar SDP ta dauki Gabam, madadin dan takarar mataimakin kujerar shugaban kasa

Babban lauyan ya kuma yi kira ga Alkalai da kuma hukumar sa ta Shari'a, kan kauracewa duk wata harkalla ta magudi ko rashin gaskiya musamman cin hanci da rashawa a yayin kare martabar kawunan su da kuma ta kasa baki daya.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, tsagwaran soyayya ta sanya wata Mata da afka cikin kabarin mijinta domin hana binne gawarsa da ya riga mu gidan gaskiya makonni biyu da suka gabata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel