Gwamnatin Buhari ta samar da zaman lafiya a Najeriya – Sakataren APC

Gwamnatin Buhari ta samar da zaman lafiya a Najeriya – Sakataren APC

Mun samu labari cewa jiya Jam’iyyar APC mai mulki ta dura kan Shugaban babban Jam’iyyar hamayyar Najeriya watau PDP wanda ta rike Kasar na tsawon shekaru har 16 a game da sha’anin tsaron Kasar.

Gwamnatin Buhari ta samar da zaman lafiya a Najeriya – Sakataren APC

Sakataren yada labarai na APC Lanre Issa-Onilu yayi wa Uche Secondus raddi
Source: Facebook

Jam’iyyar APC tayi ikirarin cewa yanzu an fi samun zaman lafiya a Najeriya a kan lokacin da PDP ta ke mulkin kasar nan. Sakataren yada labarai na APC na kasa, Malam Lanre Issa-Onilu, ya bayyana wannan a wani jawabi da yayi a Abuja.

Sakataren yada labarai na Jam’iyyar yayi wannan jawabi ne a lokacin da yake maida martani ga Jam’iyyar PDP mai adawa bayan tace sha’anin tsaro ya tabarbare a Gwamnatin Buhari. Jami’in na APC yace Jam’iyyar PDP tayi karya.

Lanre Issa-Onilu yace ikirarin da Shugaban Jam’iyyar PDP, Uche Secondus yayi na cewa an kashe mutane a mulkin Buhari fiye da yadda aka kashe Bayin Allah a lokacin yakin basasa da aka yi tsakanin 1967 zuwa 1970 ba gaskiya bane.

KU KARANTA: Dalilin da ya sa rikicin Boko Haram ya ki cinyewa inji wani tsohon Jami’in tsaro

Malam Issa-Onilu yace Uche Secondus na kokarin yi wa al’umma karya ne tare da yunkurin mantar da su abin da ya faru a lokacin da PDP ta ke mulkin Najeriya. Issa-Onilu yace PDP na kokarin siyasantar da kashe-kashen da ake yi a kasar.

Sakataren na APC yace bayan hawan Shugaba Buhari kan karagar mulki, an ci karfin Boko Haram, illa iyaka ‘Yan hare-haren kunar bakin-wake da ake yi a labe. Jam’iyyar tace Shugaba Buhari yana bakin kokarin kawo karshen matsalar tsaro.

Onilu yake cewa har wa yau, Gwamnatin Shugaba Buhari ce ta kawo karshen rikicin Yankin Neja-Delta a cikin shekaru uku da rabi. Onilu ya kuma ce a lokacin da PDP ta ke mulki ne aka rika hallaka ‘Yan siyasa tare da kashe wasu Bayin Allah.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel