Shekaru 3: Gwamnatin Buhari bata kashe ko sisi ba a kan matatun man kasar nan - Minista mai

Shekaru 3: Gwamnatin Buhari bata kashe ko sisi ba a kan matatun man kasar nan - Minista mai

Karamin ministan albarkatun man fetur na kasar Najeriya Mista Ibe Kachikwu ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari har yanzu bata zuba ko da kwandalar ta ba a cikin matatun man fetur din kasar nan.

A cewar Ministan, wannan ko shakka babu wata nasara ce da gwamnatin ta samu amma wadda al'ummar kasa ba su maida hankali a kai ba musamman idan aka yi la'akari da gwamnatocin ba.

Shekaru 3: Gwamnatin Buhari bata kashe ko sisi ba a kan matatun man kasar nan - Minista mai

Shekaru 3: Gwamnatin Buhari bata kashe ko sisi ba a kan matatun man kasar nan - Minista mai
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Ministan Buhari ya caccaki dattawan Arewa

Legit.ng Hausa ta samu cewa Ministan ya kuma bayyana cewa akalla gwamnatocin baya sun kashe kusan Naira biliyan 264 a kowace shekara wajen gyara matatun man amma daga karshe haka bata cimma ruwa ba.

Amma a cewar sa, gwamnatin nan ta shugaba Buhari ta duba hanya mafi sauka da kuma magance hakan inda yanzu tuni sun yi nisa wajen shire-shiren su na cefanar da matatun man ga 'yan kasuwa.

A wani labarin kuma, Karamin ministan albarkatun man fetur a Najeriya Mista Ibe Kachikwu a ranar Alhamis din da ta gabata ya bayyana cewa indai ana so kasar nan ta zauna lafiya musamman a bangaren yalwa da arzikin mai to dole sai gwamnati ta cire tallafin da take bayarwa.

Mista Kachikwu ya bayyana hakan ne a garin Abuja lokacin da yake gabatar da jawabin sa wajen bayar da kyaututtuka ga zakukran ma'aikatan ma'aikatan hukumar sa da nasarorin da suka samu a cikin shekaru 3.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel