Gwamma da akai: Na ji dadi sosai da majalisar dattawa suka ki tabbatar da ni - Ibrahim Magu

Gwamma da akai: Na ji dadi sosai da majalisar dattawa suka ki tabbatar da ni - Ibrahim Magu

Mukaddashin hukumar nan dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) a takaice, Ibrahim Magu ya ce shi yaji dadi sosai da majalisar dattawa ta ki amincewa da shi a matsayin tabbataccin shugaban hukumar ta EFCC.

Ibrahim Magu ya yi wannan ikirarin ne a wata kotu, jihar Legas gaban alkali lokacin da yake bayar da shaida akan wata karar da ya shigar yana kalubalantar wata jarida da yace tayi masa kazafi.

Gwamma da akai: Na ji dadi sosai da majalisar dattawa suka ki tabbatar da ni - Ibrahim Magu

Gwamma da akai: Na ji dadi sosai da majalisar dattawa suka ki tabbatar da ni - Ibrahim Magu
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Kun san yawan gidajen Magu a Abuja?

Legit.ng Hausa ta samu cewa Mista Magu ya bayyana cewa ko shakka babu yasan irin namijin kokarin da yake yi a matsayin sa na mukaddashin hukumar EFCC yana na da nasaba da kin tabbatar da shi da majalisar ta dattawa tayi.

Ya kara da cewa ya san watakila da sun tabbatar da shi da kokarin sa a matsayin shugaban hukumar bai kai yadda yake ba a yanzu.

A wani labarin kuma, Gwamnatin tarayyar Najeriya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari yanzu haka ta na aiki ba dare-ba rana don ganin ta soma biyan mafi karancin albashi na Naira dubu 30 nan ba da dadewa, kamar dai yadda Sakataren gwamnatin tarayya Mista Boss Mustapha ya fada.

Mista Mustapha mun samu cewa ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis din da ta gabata a lokacin da yake tsokaci a wajen taron goganni-in-goge ka karo na 25 da hukumar kayyade albashin ma'aikata watau national salaries, incomes and wages commission (NSIWC) ta shirya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel