Albishirin ku ma'aikata: Ga sabon sako daga fadar shugaban kasa game da karin albashi

Albishirin ku ma'aikata: Ga sabon sako daga fadar shugaban kasa game da karin albashi

Gwamnatin tarayyar Najeriya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari yanzu haka ta na aiki ba dare-ba rana don ganin ta soma biyan mafi karancin albashi na Naira dubu 30 nan ba da dadewa, kamar dai yadda Sakataren gwamnatin tarayya Mista Boss Mustapha ya fada.

Mista Mustapha mun samu cewa ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis din da ta gabata a lokacin da yake tsokaci a wajen taron goganni-in-goge ka karo na 25 da hukumar kayyade albashin ma'aikata watau national salaries, incomes and wages commission (NSIWC) ta shirya.

Albishirin ku ma'aikata: Ga sabon sako daga fadar shugaban kasa game da karin albashi

Albishirin ku ma'aikata: Ga sabon sako daga fadar shugaban kasa game da karin albashi
Source: Facebook

KU KARANTA: Matsayin Ali Nuhu a rayuwa ta - Nafisa Abdullahi

Legit.ng Hausa ta samu har ila yau cewa Sakataren gwamnatin wanda babban Sakataren din din din na ofishin sa ya wakilta, ya kara da cewa yanzu haka dai dukkan tsare tsare sun yi nisa a game da hakan kuma a kwanan nan ne ma'aikatan za su dara.

A wani labarin kuma, Mukaddashin hukumar nan dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) a takaice, Ibrahim Magu ya ce shi yaji dadi sosai da majalisar dattawa ta ki amincewa da shi a matsayin tabbataccin shugaban hukumar ta EFCC.

Ibrahim Magu ya yi wannan ikirarin ne a wata kotu, jihar Legas gaban alkali lokacin da yake bayar da shaida akan wata karar da ya shigar yana kalubalantar wata jarida da yace tayi masa kazafi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel