Gwamnatin Buhari ta na muzgunawa 'Yan PDP babu gaira babu dalili – Timi Frank

Gwamnatin Buhari ta na muzgunawa 'Yan PDP babu gaira babu dalili – Timi Frank

- Wani tsohon Kakakin Jam’iyyar APC ya nemi a ja-kunnen Shugaba Buhari

- Frank ya koka da yadda Gwamnatin Buhari ta ke hana ‘Yan adawa sakat

- Timi Frank yayi kira ga Kasashen Duniya su takawa Buhari burki tun wuri

Gwamnatin Buhari ta na muzgunawa 'Yan PDP babu gaira babu dalili – Timi Frank

Kwamared Timi Frank yana zargin Gwamnatin Buhari da zalunci a Najeriya
Source: Depositphotos

Tsohon Mai magana da yawun bakin Jam’iyyar APC mai mulki, Timi Frank yayi kira ga Kasashen ketare su gargadi Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari a game da irin muzgunuwa ‘Yan adawa da Gwamnatin sa ta ke yi a daf da zaben 2019.

Timi Frank wanda yanzu yana tare da babbar Jam’iyyar hamayya ta PDP, ya bayyana cewa ana nema a kai su bango a Najeriya, don haka akwai bukatar Kasashen waje su sa baki domin gudun ‘Yan adawa su yi wa Gwamnatin kasar mummunan bore.

KU KARANTA: Shugaban INEC ya tabbatar ‘Yan gudun Hijira za su kada kuri’a a zaben 2019

Kwamared Frank yayi kira ga Kasashen waje da su ja kunnen Shugaban kasar ya daina cin zarafin ‘Yan adawa tare da yi masu barazana iri-iri yayin da ake shiryawa zaben 2019. Frank yayi wannan kira ne a jiya Alhamis a Birnin Tarayya Abuja.

Tsohon babban Jami’in na Jam’iyyar APC yayi tir da binciken da aka shiga har gida da aka yi wa ‘Ya ‘yan ‘Dan takarar PDP Atiku Abubakar da kuma garkame wani fitaccen ‘Dan adawa, Dr. Doyin Okupe da ake yi na tsawon kwana da kwanaki.

Frank ya kuma koka game da yadda Hukumomin Kasar su ka rufe akawun din ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP, Peter Obi. ‘Dan adawar ya kuma nemi Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan sabon kudirin zaben kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel