Sai fa an cire tallafin man fetur ko Najeriya na zaunawa lafiya - Ministan albarkatun mai

Sai fa an cire tallafin man fetur ko Najeriya na zaunawa lafiya - Ministan albarkatun mai

Karamin ministan albarkatun man fetur a Najeriya Mista Ibe Kachikwu a ranar Alhamis din da ta gabata ya bayyana cewa indai ana so kasar nan ta zauna lafiya musamman a bangaren yalwa da arzikin mai to dole sai gwamnati ta cire tallafin da take bayarwa.

Mista Kachikwu ya bayyana hakan ne a garin Abuja lokacin da yake gabatar da jawabin sa wajen bayar da kyaututtuka ga zakukran ma'aikatan ma'aikatan hukumar sa da nasarorin da suka samu a cikin shekaru 3.

Sai fa an cire tallafin man fetur ko Najeriya na zaunawa lafiya - Ministan albarkatun mai

Sai fa an cire tallafin man fetur ko Najeriya na zaunawa lafiya - Ministan albarkatun mai
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Buhari ya nada sabon ministan muhalli

Legit.ng Hausa ta tsinkayi ministan yana cewa "ya zama dole gwamnati ta iya lalubo hanyoyin da zata wadata al'ummar ta da albarkatun man a hannu daya sannan kuma a dayan hannun ta fidda hannun ta daga dukkan harkar domin ba 'yan kasuwa dama."

Sannan ya kara da cewa idan har ba haka aka yi to fa lallai akwai sauran rina a kaba dangane da magance matsalolin da suka addabi hukumar.

A wani labarin kuma, Karamin ministan albarkatun man fetur na kasar Najeriya Mista Ibe Kachikwu ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari har yanzu bata zuba ko da kwandalar ta ba a cikin matatun man fetur din kasar nan.

A cewar Ministan, wannan ko shakka babu wata nasara ce da gwamnatin ta samu amma wadda al'ummar kasa ba su maida hankali a kai ba musamman idan aka yi la'akari da gwamnatocin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel