NEC: Yemi Osinbajo zai jagoranci babban taron tattalin arziki yau

NEC: Yemi Osinbajo zai jagoranci babban taron tattalin arziki yau

Mun samu labari cewa Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo zai ja ragamar taron NEC na Majalisar tattalin arzikin Najeriya. Za ayi taron ne a yau Juma’a 14 ga Watan Disamban nan da safe.

NEC: Yemi Osinbajo zai jagoranci babban taron tattalin arziki yau

Yemi Osinbajo zai gana da Gwamnoni a Vill an jima
Source: Depositphotos

Wani Hadimin Mataimakin Shugaban kasar a kan harkokin sadarwa, Mista Arukaino Umukoro, ya bayyana mana cewa Yemi Osinbajo zai jagoranci taron NEC da safiyar Juma’ar nan a ofishin tsohon babban dakin taro na Banquet Hall.

A wannan taro na musamman da za ayi a fadar Shugaban kasa na Aso Villa a cikin babban Birnin Tarayya Abuja, zai kunshi dukkanin Gwamnonin Najeriya, da kuma Gwamnan babban bankin Najeriya na CBN watau Godwin Emefiele.

KU KARANTA: Asusun Gwamnatin Najeriya ya soma kukan karancin kudi

Majalisar za ta tattauna ne game da tsare-tsare da manufofin Gwamnatin Buhari masu taba rayuwar al’umma. Manyan batutuwan da za ayi magana a kai sun hada da kiwon lafiya, harkar ilmi da sauran su. Za a soma taron ne da karfe 9:00.

Wannan shi ne babban taron da Mataimakin Shugaban kasar zai yi bayan dawowar sa Najeriya jiya. A Ranar Lahadi ne Yemi Osinbajo ya tafi Kasar Jamus inda daga nan ya wuce Kasar Ingila, ya kuma tsaya wani taro da aka yi a Masar.

Taron na NEC ya kan kunshi Gwamnonin da ba su wuce 4 bane, da kuma wasu tsirarrun Ministoci da kuma wadanda ke da ta cewa a bangaren tattalin arzikin kasar. Wannan karo kuwa za ayi zaman ne da duka Gwamnonin Jihohin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel