Kungiyar CAN ba ta tayi wa kowane ‘Dan takara mubaya’a ba - Ayokunle

Kungiyar CAN ba ta tayi wa kowane ‘Dan takara mubaya’a ba - Ayokunle

– Kungiyar CAN ta musanya rade-radin cewa tana tare da APC a zaben 2019

– Shugaban Kiristocin Kasar yace ba su tare da ‘Dan takara a zabe mai zuwa

– Rabaren Ayokunle yayi magana game da babban zaben da za ayi a Najeriya

Kungiyar CAN ba ta tayi wa kowane ‘Dan takara mubaya’a ba - Ayokunle

Shugaban CAN yace babu ruwan su da goyon bayan wani 'Dan takara
Source: UGC

A daidai lokacin da babban zaben 2019 a Najeriya yake karasowa, Kungiyar Kiristocin Najeriya watau CAN ta karyata rahotannin da ke yawo na cewa tana tare da tazarcen Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ke Jam’iyyar APC mai mulki.

Rabaren Samson Ayokunle wanda shi ne Shugaban Kiristocin Najeriya yayi karin haske game da ganawar da su kayi da ‘Yan takarar Shugaban kasa a zaben 2019. Rabaren Ayokunle yace Kungiyar ba ta nuna goyon baya ga kowane ‘Dan takara.

KU KARANTA: ‘Yan gudun Hijira za su kada kuri’a a zaben 2019 - INEC

Shugaban na CAN yayi wannan jawabi ne ta bakin wani babban Hadimin sa kan sadarwa watau Fasto Adebayo Oladeji. Kungiyar CAN tace a zaman da tayi da ‘Yan takara, ba ta nuna goyon baya ga Shugaban kasa Buhari domin ya zarce a ofis ba.

Kiristocin Kasar sun nuna cewa ba za su shiga cikin rigimar siyasa ba, illa iyaka kawai su na kira ayi zabe na gaskiya a 2019. Kungiyar CAN ta bakin Ayokunle ta kuma nemi ‘Yan Majalisa su yi aiki da Shugaban kasa game da sabon kudirin zaben kasar.

Kwanan nan ne CAN ta gana da masu neman mulkin Najeriya a zabe mai zuwa. Daga cikin wadanda Kungiyar ta zauna da su akwai ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa a PDP, Peter Obi, da kuma Obi Ezekwesili da wasu wakilai daga Jam'iyyar APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel