Wata sabuwa: Shugaban majalisar dattawa ya shiga rudani kan takamaimen adadin Sanatocin Najeriya

Wata sabuwa: Shugaban majalisar dattawa ya shiga rudani kan takamaimen adadin Sanatocin Najeriya

Da alama yawan sauye sauyen jam’iyyu da yan siyasan Najeriya ke yi a duk lokacin da suka ga dama ya fara haifar da rudani, inda ko a yayin zaman majalsar dattawan Najeriya na ranar Alhamis sai da lissafi ya kwace ma Sanatocin akan takamaimen adadinsu.

Wannan cece kuce ya faru ne tsakanin mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Ike Ekweremadu wanda ya jagoranci zaman majalisar na ranar Alhamis, 13 ga watan Disamba, da kuma shugaban masu rinjaye, Sanata Ahmad Lawan.

KU KARANTA: Sabon rikici tsakanin yan majalisa da shugaban kasa: Ministan Buhari ya debo ruwan dafa kansa

Wata sabuwa: Shugaban majalisar dattawa ya shiga rudani kan takamaimen adadin Sanatocin Najeriya

Majalisar Sanatocin Najeriya
Source: Depositphotos

Majiyar Legit.com ta ruwaito Sanata Ahmad Lawan ne ya mike don yayi ma takwarorinsa jawabi game da wani rahoto da yace ya gani a jaridar Daily Trust dake bayyana adadin Sanatocin majalisar dattawa gaba daya, inda rahoton yace PDP ta fi APC yawan Sanatoci.

“Jaridar Daily Trust na ranar Alhamis a shafi na 57 ta ruwaito wai adadin Sanatocin APC shine 57, yayin da Sanatocin PDP suka kai 58, don haka wannan rahoto ba gaskiya bane, ingantaccen adadin Sanatocin gidannan shine APC na da Sanatoci 56, PDP kuma nada Sanatoci 46” Inji shi.

Sai dai jagoran zaman majalisar a ranar Alhamis, Sanata Ike Ekweremadu ya bayyana rashin amincewarsa da lissafin Sanatocin jam’iyyar APC dana jam’iyyar PDP da Ahmad Lawan ya bayar, inda yace a yanzu babu wanda yasan Sanatocin kowacce jam’iyya.

“Game da batun adadin Sanatocin kowacce jam’iyya, bamu da wannan alkalumman a yanzu haka.” Inji Sanata Ike Ekweremadu.

A hannu guda kuma, Ahmad Lawan ya janyo hankalin majalisa ga rahoton da jaridar ta buga na cewa wai Sanatoci basu amince da nadin kaakakin yakin neman zaben shugaba Buhari, Festus Keyamo a hukumar gudanarwar NDIC ba, wai Sanata Ekeremadu ne kawai ya dannesu.

“Maganr gaskiya shine a zuwan farko daka fara tambayar Sanatoci game da amincewarsu ko akasin haka da nadin Festus Keyamo ba’a samu takamaimen muryar da tafi karfi tsakanin wadanda suka amince da wadanda basu amince ba, har sai da ka sake tambayar ne aka samu wadanda suka amince suka fi rinjaye.” Inji Lawan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel