Sabon rikici tsakanin yan majalisa da shugaban kasa: Ministan Buhari ya debo ruwan dafa kansa

Sabon rikici tsakanin yan majalisa da shugaban kasa: Ministan Buhari ya debo ruwan dafa kansa

Yan majalisar wakilan Najeriya sun nemi wani minista daga cikin ministocin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari daya fito a fili ya basu hakuri tare da neman gafararsu bisa wasu maganganu daya furta akan majalisar.

A cewar yan majalisar, maganganun da Ministan ya furta akansu bai dace ba, kuma ba gaskiya bane, don haka basu ji dadin maganganun ba, da wannan ne suke kira a gareshi yayi gaggawar janye maganganun tare da neman afuwansu.

KU KARANTA: Dansanda ya bindige wani direban babbar mota har lahira a jahar Legas akan N1000

Sabon rikici tsakanin yan majalisa da shugaban kasa: Ministan Buhari ya debo ruwan dafa kansa

Majalisa
Source: Depositphotos

Majiyar Legit.com ta ruwaito wani dan majalisa daga jahar Neja, Abubakar Chika Adamu ne ya fara tayar da maganar a zaman majalisar na ranar Alhamis 13 ga watan Disamba, inda yace wajibi ne Ministan kasafin kudi da tsare tsare, Udo Udoma ya nemi afuwan majalisa.

Dan majalisa Adamu ya zarg ministan ne da furta wasu kalamai dake nufin majalisun dokokin Najeriya ne suke jan kafatare da zargin kokarin yin kafar angulu ga bukatar da shugaban kasa ya mika ma majaliar na ganin ya halarci majalisa a ranar Alhamis don mika musu kasafin kudin 2019.

Sai dai shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa ba’a ruwaito maganganun ministan daidai yadda ya furtasu ba, don amma Kaakakin majalisar, Yakubu Dogara ya bukaci a baiwa ministan dama ya yi karin gaske ko kuma ya janye maganan.

A hannu guda kuma, ma’aikatan kasafin kudi da tsare tsare ta fitar da sanarwa inda take wanke ministan daga zargin musguna ma majalisar a cikin maganganun da yayi, kamar yadda hadimin ministan, Akpandem ya bayyana.

Mista Akpandem yace babu wani lokaci koda sau daya da minista Udom ya taba furta kalaman batanci ko wani kalami dake nuna akwai rikici tsakanin majalisun dokokin Najeriya da bangaren zartarwa.

“Asali ma Ministan cewa yayi zasu bi duk wata hanyar data dace don ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2019 a gaban majalisar dokokin Najeriya.” Inji Akanpandem.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel