Dansanda ya bindige wani direban babbar mota har lahira a jahar Legas akan N1000

Dansanda ya bindige wani direban babbar mota har lahira a jahar Legas akan N1000

An kaure da hatsaniya yayin da wani dansanda sarkin tabargaza ya dirka ma wani direban babbar motan dakon man fetir harsashi akan ya hanashi kudi naira dubu daya, a jahar Legas, kamar yadda jaridar Daily trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito lamarim ya faru ne a ranar Alhamis, 13 ga watan Disamba a unguwar Trinity dake yankin Apapa ta jahar Legas, inda wani Dansanda ya bukaci direban motar dakon mai ya bashi cin hancin naira dubu daya, amma direban ya tubure sai dai ya bashi naira dari biyar.

KU KARANTA: Za’a rataye wani matashi daya daddatsa matar babansa akan zargin maita

Dansanda ya bindige wani direban babbar mota har lahira a jahar Legas akan N1000

Tanka
Source: Facebook

Wannan bani-na-hana ne ya janyo rikici tsakanin mutanen biyu, inda daga nan ya janyo cece kuce a tsakaninsu, daga nan kuma kwatsam sai Dansandan ya dirka masa harsashi, nan da nan sauran direbobi da yaran motocinsu suka harzuka har ta kai ga sun yi kokarin kashe Dansandan.

Amma fa direbobin basu kai ga cika burinsu ba kafin Yansanda su hallara, wadanda suka bude wuta da harbi a sama, da haka ne kowa yace kafa idan baki yi bani waje, da haka suka ceci Dansandan.

Sai dai duk da haka, direbobi da yaran motocinsu sun gudanar da zanga zangar nuna bacin ransu da yadda Yansanda ke wulakatansu a Legas, inda suka gicciye motocinsu suka tare hanya dasu, tare da kona tayoyin mota akan titin.

Wannan zanga zanga da direbobin suka gudanar ya baiwa yan iskan gari da aka fi sani da ‘Area boys’ daman fasa shagunan yan kasuwa tare da yi ma jama’a kwacen kudi da wayoyi, sa’annan sun afka ma wasu mutane inda suka raunatasu tare da farfasa gilasan motocin jama’a.

Wani direba mai suna Danladi Usman ya bayyana cewa ana cutansu dayawa a Legas, musamman ma daga jami’an tsaro; “Muna biyan Yansanda N1000, muna biyan Sojojin ruwa N3000, muna biyan jami’an hukumar LASTMA, jami’an kananan hukumomi da yan isakn gari, abin yayi yawa har kashemu suna yi.”

Shima Kaakakin rundunar Yansanda jahar Legas yace bai samu cikakken rahoto game da rikicin ba, amma ya tabbatar da faruwar rikici a yankin Apapa kuma an kashe mutu daya, sai dai yace kwamishinan Yansandan jahar ya kaddamar da bincike akan lamarin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel