Babban magana: Mun kammala shirin mika matatun man Najeriya ga yan kasuwa – Buhari

Babban magana: Mun kammala shirin mika matatun man Najeriya ga yan kasuwa – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa hukumar man fetir ta Najeriya, NNPC, ta kammala aikin zaban wasu kamfanonin yan kasuwa da suka kware wajen aikinsu don mika musu duka matatun man Najeriya da zummar su yi ma matatun aikin garambawul.

Buhari ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da ya karbi bakoncin sabbin shuwagabannin kungiyar ma’aikatan sashin danyen mai da gas a fadar gwamnatin Najeriya dake babban birnin tarayya Abuja yayin wata ziyara da suka kai masa.

KU KARANTA: Za’a rataye wani matashi daya daddatsa matar babansa akan zargin maita

Babban magana: Mun kammala shirin mika matatun man Najeriya ga yan kasuwa – Buhari

Buhari da yan NUPENG
Source: Facebook

Majiyar Legit.com ta ruwaito Buhari yana cewa gyare gyare da sauya dokokin bangaren al’amuran da suka shafi harkar mai da gas a Najeriya na da matukar muhimmanci, don haka duk wanda ya san muhimmancin haka ba zai so ayi gaggawa cikin aikin ba idan har ana son fidda A’I daga rogo.

“A game da matatun manmu, mun yanke shawarar bin tsarin hadin gwiwa da yan kasuwa masu zuba hannyen jari, sai dai hakan ya dauki tsawon lokaci fiye da yadda muka tsammani a farko. Amma na samu labarin NNPC ta gama aikin zabo kwararrun kamfanonin da zasu gudanar da gyararrakin.

“Haka zalika ina da labarin cewa a yanzu suna kan gabar tattauna yadda za’a samar da kudaden aikin ne, wanda da zarar sun kammala za’a fara gudanar da aikin gyare gyare a dukkanin matatun man na Najeriya.” Inji Buhari, kamar yadda jaridar Daily trust ta ruwaito.

Shugaban ya tabbatar ma shuwagabannin NUPENG burinsa na cigaba da tallafa ma sabbin hikimomi ta yadda za’a ciyar da bangaren man fetir a Najerya gaba, don haka ya bayyana musu cewa kofarsa a bude take don karbar shawarwari akan yadda za’a samar da sabbin matatun mai na yan kasuwa a Najeriya.

Daga karshe Buhari ya bayyana ma bakinnasa cewa yana daya daga cikin wadanda suka haifar da dokar yin amfani da kamfanonin gida wajen gudanar da aiki a bangaren harkar man fetir a Najeriya, don haka Najeriya zata cigaba da saka kamfanonin gida a harkar mai a duk inda suke da kwarewa akai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel