Kabilar Igbo, baza ta sake yarda 'yan takara su yaudare ta ba kan 2023

Kabilar Igbo, baza ta sake yarda 'yan takara su yaudare ta ba kan 2023

- Atiku Abubakar yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai cika alkawari ba a 2023

- A bayyane yake cewa APC na yaudarar kabilar Igbo

- Ya dauki abokin takara ne daga inyamurai saboda yana musu fatan alheri

ASUU na sake gargadin komawa yajin aiki a jami'o'in kasar nan

ASUU na sake gargadin komawa yajin aiki a jami'o'in kasar nan
Source: Depositphotos

Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma Dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP, yace shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar APC ba zai karrama alkawarin da yayi da kudu maso gabas ba na samar da shugaban kasa a 2023 Idan har suka bashi goyon baya wajen cin zaben shekara mai zuwa.

Yace a bayyane yake APC na yaudarar inyamurai ne saboda fadar shugaban kasa ta bakin sakataren Gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, na cewa shugabancin kasa zai koma yankin kudu maso gabas a 2023.

Babatunde Fashola, Ministan wuta, aiyuka da gidaje yace 2023 lokaci ne da yankin kudu maso yamma zasu karbi mulki.

Atiku wanda yayi maganar ta bakin Segun Sowunmi, mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben shi, yace Buhari da jam'iyyar shi a cikin shekarun nan sun nuna basu rike alkawari, wanda hakan ya bayyana ne a jerin alkawarirrikan da suka yi wa yan Najeriya a yakin neman zaben shi na 2015 amma har yanzu basu cika ba.

DUBA WANNAN: Labarin mahaifi da dansa masu kwanciya da diyarsa

Yace a maimakon yin alkawarin da bazai cika ba kamar APC, ya nuna yan ma inyamurai fatan alheri tunda abokin takarar shi, Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra ma daga cikin su yake.

"Bai kamata ace an kara yarda dashi ba, Kuna tunanin zai cika alkawari ne a 2023? A wani bangare, fadar shugaban kasa ta yaudare su da cewa mulki zai koma gurin su a 2023 Idan suka goyi bayan Buhari. A wani bangaren kuma, Ministan wuta, aiyuka da gidaje ya sanar dasu cewa mulki zai koma kudu maso yamma ne a 2023. Yan Najeriya sun fi su wayau. "

"Kabilar Igbo suna da wayau fiye da yanda suke tunani. Atiku kuwa ya basu dama ta hanyar basu gurbin mataimakin shugaban kasa, Peter Obi. Tabbas idan yayi da kyau, akwai yuwuwar kudu maso gabas ta samu damar shugabancin kasa, kuma zai goyi bayan su."

Atiku yace a maimakon tada jijiyoyin wuya akan wanda zai shugabancin kasar a 2023, yan Najeriya su maida hankali wajen gyara kasar ta yadda kowanne yanki zai samu cigaba.

Yayi alkawarin ba wa kananan hukumomi yancin su ta yanda zasu samu isassun kudaden da zasu habaka kansu daga tushe.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel