Zaben 2019: Ministan Buhari yayiwa dattijon Arewa, Farfesa Ango wankin babban bargo

Zaben 2019: Ministan Buhari yayiwa dattijon Arewa, Farfesa Ango wankin babban bargo

Daya daga cikin ministoci a gwamnatin shugaba Buhari kuma mai kula da ma'aikatar wasanni da matasa, Barista Solomon Dalung ya mayar wa da kungiyar dattawan arewa da martani, inda ta ce su kama girmansu.

Idan mai karatu bai manta ba dai a farkon mako ne shugaban kungiyar na dattawan arewa watau Nother Elders Forum a turance Farfesa Ango Abdullahi ya yi kira ga mutanen yankin da kada su sake zaben Buhari a 2019 domin a cewar sa bai tsinana komai ba.

Zaben 2019: Ministan Buhari yayiwa dattijon Arewa, Farfesa Ango wankin babban bargo

Zaben 2019: Ministan Buhari yayiwa dattijon Arewa, Farfesa Ango wankin babban bargo
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Ba bu wanda ya so Buhari kamar ni - Kwankwaso

Legit.ng Hausa sai dai ta samu cewa yayin da yake mayar da martani a hirarsa da majiyar mu, Solomon Dalung ya ce ba irin wadannan kalaman ba ne suke bukata daga wajen dattawan ba.

Ya kara da cewa Farfesa Ango Abudllahi, yana da jikoki, sun masa yawa saboda haka bai ma san abin da ke faruwa ba a arewa. Wannan kuskure da suka ce sun gani mu ba mu gan shi ba.

Ya ce kila ya dade Farfesan bai fita waje ba balle ya san halin da arewa take ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel