Da duminsa: Dan majalisar tarayya daga Katsina ya fice daga APC ya koma PDP

Da duminsa: Dan majalisar tarayya daga Katsina ya fice daga APC ya koma PDP

Ibrahim Murtala, dan majalisar wakilai na tarayya daga jihar Katsina mai wakiltan mazabun Munsawa/Matazu ya fice daga jam'iyyar APC ya koma PDP.

Sanarwar sauya shekar Murtala yana cikin wata wasika ne da kakakin majalisa, Yakubu Dogara ya karanto a zauren majalisar a lokacin da aka fara zaman majalisar na yau Talata kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Yanzu-yanzu: Dan majalisar Katsina ya sauya sheka daga APC zuwa PDP
Yanzu-yanzu: Dan majalisar Katsina ya sauya sheka daga APC zuwa PDP
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yadda na lashe zaben shugabancin kasa na 2015 - Buhari

A cikin wasikar, Murtala ya bayyana cewa ya yi farin cikin ficewa da jam'iyyar APC saboda rikice-rikicen da ya yiwa jam'iyyar katutu ya koma PDP.

Sanarwar ficewar Murtala daga jam'iyyar APC zuwa PDP ya sanya mambobin majalisar na jam'iyyar PDP sunyi tafi tare da yin kirarin jam'iyyar PDP a majalisar na tsawon minutan biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel