Shugaba Buhari ya aikawa Nuhu Ribadu sako bayan ya lashe lambar yabo

Shugaba Buhari ya aikawa Nuhu Ribadu sako bayan ya lashe lambar yabo

A karshen makon jiya ne aka ba tsohon Shugaban Hukumar EFCC ta Najeriya watau Nuhu Ribadu lambar yabo a wata Kasar Asiya. Wannan ya sa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya sa murna.

Shugaba Buhari ya aikawa Nuhu Ribadu sako bayan ya lashe lambar yabo
Kungiyar Hamad Al Thani International Anti-Corruption Excellence ta karrama Ribadu
Asali: Twitter

NAN ta Najeriya ta bayyana cewa wata Kungiyar Kasar waje mai yaki da satar dukiyar Gwamnati mai suna “Sheikh Tamin Bin Hamad Al Thani International Anti-Corruption Excellence” (ACE) ta karrama Nuhu Ribadu a Ranar Juma’a.

Kungiyar ta kasar UAE ta ba Shugaban Hukumar EFCC na Najeriya, Nuhu Ribadu wannan lambar girma ne saboda irin kokarin da yayi wajen yakar Miyagun barayi a Najeriya a lokacin yana rike da EFCC shekaru kusan 10 da su ka wuce.

Mai magana da bakin Shugaban Najeriya Buhari watau Mista Femi Adesina ya fitar da jawabi na musamman washegari watau a Ranar Asabar inda Shugaban kasar ya taya Nuhu Ribadu murnar samun wannan lambar yabo da girma.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta nemi ta cafke wani na-kusa da Atiku Abubakar

Muhammadu Buhari yace zaben Ribadu da aka yi tare da wasu mutane 7 ya nuna irin kokarin da yayi wajen magance matsalar satar dukiyar al’umma a Najeriya. Shugaban kasar yace wannan yana cikin muradin Gwamnatin sa ta APC.

A jawabin Shugaban kasar, yayi kira ga Shugaban EFCC da sauran masu yakar Barayi a Najeriya, da su cigaba da tsaya tsayin-daka wajen aikin su, ba tare da jin tsoron ‘Yan adawa da ke kokarin kawo masu cikas ta hanyoyi daban-daban ba.

Shugaban Najeriya, Buhari ya bayyana cewa kyautar da aka ba Shugaban EFCC na farko,Nuhu Ribadu a Kasar Malaysia ya nuna cewa dole ayi maganin masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel