Osinbajo ya kaddamar da yakin neman zabe na gida-gida a jihar Legas

Osinbajo ya kaddamar da yakin neman zabe na gida-gida a jihar Legas

- Mataimakin shugaban kasa ya kaddamar da wani salon yakin neman zaben shugaban Buhari na gida-gida a jihar Legas

- Osinbajo ya yi kira kan haramtawa jam'iyyar PDP komawa kujerar mulkin kasar nan

- Tsohon Malamin Jami'ar jihar Legas ya fayyace babbar matsala ta rashawa da ke fuskantar Najeriya

A yau Asabar, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, yayin bayyana nagartar shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kuma kaddamar da yakin neman zabe na gida-gida cikin babban birni na jihar Legas.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, al'ummar Najeriya kada su taba tsammanin shugaban kasa Buhari zai saci dukiyar su, kuma haka zalika ba za ya taba bari a dasa wawa a kan ta. Ya ce wannan shine kadai ne bambancin sa da sauran masu hankoron kujerar shugaban kasa a zaben 2019.

A yayin tsarkake shugaban kasa Buhari da kuma kadaita shi ta hanyar jingina masa kyakkyawar dabi'a da kuma akidar gaskiya da rikon amana, Osinbajo ya bayyana cewa wannan akida ita kadai ce za ta fidda Najeriya zuwa tudun tsira da aminci.

Osinbajo ya kaddamar da yakin neman zabe na gida-gida a jihar Legas

Osinbajo ya kaddamar da yakin neman zabe na gida-gida a jihar Legas
Source: Facebook

Kamar yadda majaiyar jaridar Legit.ng ta ruuwaito, mataimakin shugaban kasar ya yi wannan furuci yayin kaddamar da yakin neman zabe na gida zuwa gida, da a cewarsa tasirin hakan shine mafifici wajen isar da kudirirrika da kuma manufofi gami da tsare-tsaren da gwamnatinsu da tanada domin ci gaban kasa baki daya.

Osinbajo ya kuma gargadi 'yan Najeriya akan hatsarin da ke tattare da jam'iyyar adawa ta PDP, inda ya bayyana cewa ko shakka ba bu mantuwa ba za ta kusanci tarihin da jam'iyyar ta kafa ba tsawon 16 a kujerar mulki.

KARANTA KUMA: Ba za mu shiga yajin aiki ba - PENGASSAN, NUPENG

Tsohon lauyan kolu kuma kwamishinan shari'a na jihar Legas ya kara da cewa, rashawa ita ce mafi kololuwar barazana da ke fuskanta kasar nan a halin yanzu da ya kamata al'ummar Najeriya su dawwama akan haramtawa barayi komawa kan karagar mulkin kasar nan.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, Osinbajo ya kuma ziyarci wasu yankuna da ke karkashin karamar hukumar Ikeja a jihar ta Legas domin neman goyon bayan su yayin da babban zabe ya gabato.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, badakalar rashawa ta tsohuwar Ministan man fetur, Diezani Alison Madueke, ta shafi wasu manyan 'yan siyasa biyu a jihar Adamawa da tuni hukumar yaki da rashawa ta gurfanar da su gaban Kuliya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel