Babban lauya Keyamo ya fadi dalilin da yasa wasu ke yada labarin an musanya Buhari

Babban lauya Keyamo ya fadi dalilin da yasa wasu ke yada labarin an musanya Buhari

Wata jita-jita da ta dade tana yawo a Najeriya, ita ce ta batun zargin cewar an musanya shugaba Buhari da wani mutum daga kasar Sudan bayan shugaban kasar ya mutu yayin doguwar jinyar da ya yi a kasar Ingila.

Babban lauya Festus Keyamo ((SAN), Darektan kamfen din shugaba Buhari, ya bayyana dalilin da yasa wasu mutane ke yada jita-jitar cewar shugaba Buhari ya mutu.

Keyamo ya bayyana cewar batun cewar shugaba Buhari ya mutu kuma an maye gurbinsa da wani mai suna Jubril daga kasar Sudan, duk aikin makiya Buhari ne.

Da yake magana da jaridar Sun, Keyamo ya ce, "hauka ne da kuma shakiyanci."

"Suna yin wannan izgilanci ne saboda tsagwaron tsanar su ga shugaba Buhari. Na sha bayar da misalin cewar, idan mutumin da ka tsana ya kwanta rashin lafiya, za kayi ta fatan ya mutu ko kar ya samu lafiya, musamman ma idan bokaye suka baka tabbacin cewar mutuwa zai yi. Idan mutumin ya samu lafiya, ya mike, sai ka fara tunanin ko shi kake gani a zahiri ko kuma fatalwar sa saboda tuni ka gama gamsuwa a ranka cewar ya mutu.

"To, domin mutum ya gamsar da kiyayyar sa ga wanda ba ya so, sai ya fara kirkirar duk wata karya da zata bashi kwanciyar hankalin da yake so.

"Irin wannan yanayin makiya Buhari suka tsinci kansa a Najeriya. Masu yada cewar Buhari ya mutu kuma an musanya shi, na yin hakan ne domin biyan bukatar haukan da kiyayyar Buhari ta jefa su.

"Ba zasu iya yarda cewar Buhari ya samu lafiya, ya dawo Najeriya ba, saboda kiyayyar da suke yi masa ta haukatar da su, ta rufe masu kwakwalwa, basa iya ko tunani.

"Kamar a kasar Amurka ne da wasu mutane da basa son Trump suka kasa hakuri da batun cewar ya kayar da Hillary Clinton. Irin wadannan mutane ne a kasar Amurka suka tsara fadar gwamnati a na'urar su mai kwakwalwa tare da saka Hillary a ciki. Su a wurinsu, har yanzu Hillary ce ke mulkin Amurka. Irin wannan kiyayyar ce Buhari ke fuskanta a Najeriya daga wasu tsirarun mutane," a kalaman Keyamo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel