Ba za mu shiga yajin aiki ba - PENGASSAN, NUPENG

Ba za mu shiga yajin aiki ba - PENGASSAN, NUPENG

- Kungiyoyin ma'aikatan man fetur na Najeriya sun janye kudirin su na shiga aiki

- A baya kungiyoyin sun yi barazanar shiga yajin aiki tare da bai wa gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki bakwai na cika sharuddanta

- Gwamnatin tarayya za ta sauke nauyin bashin kudade na tallafin man fetur da rataya a wuyanta

Mun samu cewa, kungiyoyin ma'aikatan hako man fetur na kasa, sun yi wasti da kudiri da kuma aniyyar su ta shiga yajin aiki bayan barazanar mamallakan rijiyoyin man fetur ta dakatar da gudanar aikace-aikace na hako ma'adanai.

Kungiyoyin sun bayyana hakan ne a yau Asabar cikin wata sanarwa da sa hannun shugabannin su, Messrs Francis John da kuma Williams Akporeha, da suka gabatar cikin babban birnin kasar nan na tarayya.

A baya dai kungiyoyi sun yi barazanar afkawa yajin aiki tare da baiwa gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki bakwai akan ta sauke nauyi bashin kudade na tallafin man fetur da ya rataya a wuyanta.

Ba za mu shiga yajin aiki ba - PENGASSAN, NUPENG

Ba za mu shiga yajin aiki ba - PENGASSAN, NUPENG
Source: UGC

Bayan aiwatar da zaman sulhu, shawarwari gami da tuntube-tuntube da wakilai na gwamnatin tarayya, kungiyoyin sun yanke shawarar watsi da kudirin su yayin da gwamnatin tarayya ta bayar da tabbacin sauke wani kaso na bashin da ke kanta gabannin ranar 14 ga watan Dasumba.

KARANTA KUMA: Ku zabi 'yan takarar da suka cancanta - Obasanjo ya shawarci ' Yan Najeriya

Cikin sanarwar da shugabannin kungiyoyin suka gabatar sun kuma bayyana cewa, ci gaban kasa da kuma inganta jin dadin ma'aikatan su ya sanya suka ayyana wannan kudiri na shiga yajin aiki a baya domin gwamnatin tarayya ta yi gaggawar waiwayar su.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, tsohowar Ministan man fetur, Diezani Alison Madueke, ta gogawa wasu manyan 'yan siyasa biyu kashin kaji na badakalar rashawa da babakere kan $115m da ake zargin ta.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel