Jihar Anambra: Rundunar 'yan sanda ta ladaftar da jami'anta 28, ta cafke 'yan kungiyar asiri 124

Jihar Anambra: Rundunar 'yan sanda ta ladaftar da jami'anta 28, ta cafke 'yan kungiyar asiri 124

- Rundunar 'yan sanda a jihar Anambra ta ce ta ladaftar da akala jami'anta 28 wadanda suka aikata laifuka daban-daban a lokacin da suke gudanar da ayyukansu

- Rundunar ta ce daga cikin hukuncin da aka yankewa jami'an da suka aikata laifin sun hada da kora daga aikin baki daya

- Haka zalika, jami'in hulda da jama'a na rundunar ya ce, rundunar ta samu nasarar cafke 'yan kungiyar asiri daga sassa daban daban na fadin jihar

A ranar Asabar, rundunar 'yan sanda a jihar Anambra ta ce ta ladaftar da akala jami'anta 28 wadanda suka aikata laifuka daban-daban a lokacin da suke gudanar da ayyukansu.

A cikin wata sanarwa daga jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda ta jihar, Haruna Mohammed, rundunar ta ce daga cikin hukuncin da aka yankewa jami'an da suka aikata laifin sun hada da kora daga aikin baki daya.

Mohammed ya ce wannan hukuncin ya biyo bayan cimma kudurin rundunar na yaki da masu cin hanci da rashawa a cikin gudanar da aikin 'yan sanda tsakanin jami'an rundunar.

KARANTA WANNAN: Makircin fadar shugaban kasa: PDP ta yi Allah-wadai da sankame asusun bankin Peter Obi

Jihar Anambra: Rundunar 'yan sanda ta ladaftar da jami'anta 28, ta cafke 'yan kungiyar asiri 124

Jihar Anambra: Rundunar 'yan sanda ta ladaftar da jami'anta 28, ta cafke 'yan kungiyar asiri 124
Source: Depositphotos

Ya ce: "Sanin kowa ne cewa karkashin jagorancin kwamishinan 'yan sanda na jihar Garba Baba Umar, akwai yaki da cin hanci da rashawa da kuma karya dokokin aikin rundunar 'yan sanda, don haka aka samar da wani sashe na musamman mai suna 'sashen karbar korafe korafe na rundunar 'yan sanda a jihar Anambra' wanda ya gudanar da bincike kan zargin da akewa jami'an, ta hanyar korafe korafen da sashen ya samu daga hannun jama'ar jihar.

"Zuwa yanzu, rundunar ta dauki matakin hukunci kan jami'ai 28 bisa kamasu da aikata laifuka daban daban, da kuma yi masu hukunci kamar na ragin matsayi, kora daga aikin kwata kwata da kuma bayar da gargadi da dai sauransu gwargwadon laifin da jami'i ya aikata."

Haka zalika, jami'in hulda da jama'a na rundunar ya ce, rundunar ta samu nasarar cafke 'yan kungiyar asiri daga sassa daban daban na fadin jihar.

Ya ce rundunar 'yan sandan ta samu wannan nasarar ne biyo bayan wani kai sumame da suka yi a wata mabuyar 'yan ta'adda da kuma wuraren aikata laifuka.

Ya ce 37 daga cikin wadanda aka cafken sun amince da wannan zargi da ake masu inda aka kaisu kotu, yayin da 53 daga cikinsu, an tantance su kana aka sake su, sai kuma 44 da har yanzu ake kan gudanar da bincike akansu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.co

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel