Hankula sun tashi bayan jirgin saman zuwa Kaduna ya samu matsala kafin yayin tashi

Hankula sun tashi bayan jirgin saman zuwa Kaduna ya samu matsala kafin yayin tashi

- Wani jirgin fasinjoji ya samu matsala yayin da ya ke kokarin tashi daga filin tashin jirage na Murtala Mohammed da ke Legas

- Matukin jirgin ya kwashe misalin mintuna 20 yana zura guda a titin tashin jiragen kafin ya juya ya sanar da fasinjojin cewa akwai matsala

- Fasinjojin sun zargi kamfanin jirgin da sakaci kuma suka mika gidiya ga Allah saboda matsalar bata afku lokacin da jirgin ke samaniya ba

Hankula sun tashi bayan jirgin saman zuwa Kaduna ya samu matsala kafin ya tashi

Hankula sun tashi bayan jirgin saman zuwa Kaduna ya samu matsala kafin ya tashi
Source: Twitter

Fasinjojin jirgin sama na Arik Air da za su taso daga Legas zuwa Kaduna sun shiga cikin dimuwa a yau Asabar yayin da jirgin saman da suke ciki ya samu matsala yayin da suke kokarin tashi daga filin jiragen samar.

Jirgin kirar Boeing 707 dai ya kamata ya dauki fasinjoji daga Legas zuwa Kaduna da Jos lokacin da matsalar da afku misalin karfe 3:15 na yamma.

Fasinjojin sun zargi kamfanin da sakaci wajen duba jiragen kafin fasinjoji su shiga ciki.

DUBA WANNAN: 2019: Atiku ya fadi abinda gwamnatinsa ba za ta yarda da shi ba idan aka zabe shi

Sai dai, sun mika godiyarsu ga Allah kan yadda matsalar da afku kafin jirgin ya tashi zuwa sararin samaniya.

Jirgin ya yi gudu a titin tashin jirgin Murtala Mohammed da ke Legas na tsawon mintuna 20 kafin matukin jirgin ya sanar da cewa jirgin ya samu matsala.

"Ina neman afuwar ku, jirgin ya samu matsala kuma akwai bukatar ayi gyra," inji direban yayin da ya juyo jirgin.n bukaci fasinjojin su sauka da jirgin su koma dakin da fasinjoji ke jiran jirgi su saurari karin bayani.

Bayan misalin sa'a guda, an samo wani jirgin daban wanda ya dauki fasinjojin Kaduna yayin da fasinjojin Jos suka cigaba da jiran tsamani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel