Ainihin dalilin da ya sa Akbabio, Obanikoro suka sauya sheka daga PDP zuwa APC – Sule Lamido

Ainihin dalilin da ya sa Akbabio, Obanikoro suka sauya sheka daga PDP zuwa APC – Sule Lamido

Tsohon gamnan Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya bayyana ainahin dalilin da ya sa wasu daga cikin manyan ‘yan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kamar su Godswill Akpabio da Musliu Obanikoro suka sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki.

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya bayyana cewa wasu manyan PDP sun koma jam’iyyar All Progressives Party (APC) ne saboda jam’iyyar na neman ta ci mutuncin su da karfin mulki

“Tun da gwamnati mai ci ta kyallara idanu ta hango irin makudan kudaden da wadannan mutane suka mallaka a asusun ajiyar su na banki sai suka yi amfani da hukumar yaki da cin hanci da rashawa suka fara bibiyan su.

“Daga nan sai suka rika yi musu barazanar ko su dawo jam’iyyar APC a yafe musu ko kuma su ci gaba da zama a PDP ayi musu tonon silili sannan a daure su."

Ainihin dalilin da ya sa Akbabio, Obanikoro suka sauya sheka daga PDP zuwa APC – Sule Lamido

Ainihin dalilin da ya sa Akbabio, Obanikoro suka sauya sheka daga PDP zuwa APC – Sule Lamido
Source: Depositphotos

Lamido ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi a filin taron kaddamar da kamfen din jam’iyyar PDP a jihar Jigawa.

KU KARANTA KUMA: Ba za mu daina fitowa ba har sai an saki Elzakzaky – Yan shi’a

Bayan nan ya roki wadanda suka canja sheka, wato suka fice daga PDP zuwa APC a dan kwanakinnan da su dawo jam’iyyar PDP.

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel