Makircin fadar shugaban kasa: PDP ta yi Allah-wadai da sankame asusun bankin Peter Obi

Makircin fadar shugaban kasa: PDP ta yi Allah-wadai da sankame asusun bankin Peter Obi

- Jam'iyyar PDP ta koka kan yadda aka dakatar da duk wasu hada hadar kudade a asusun banki mallakin Mr Peter Obi, matarsa, iyalansa da na kasuwancinsu

- PDP, ta ce tun bayan da aka bayyana Obi a matsayin abokin takarar Atiku yake samun barazana kan hakan

- Jam'iyyar ta ce APC ta tsorata da irin nasabar Peter Obi, musamman, kwarewarsa a wajen jagoranci, sanin makamar aiki da bin diddigi a aikin gwamnati

Kungiyar yakin zaben dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP (PPCO) ta koka kan yadda aka dakatar da duk wasu hada hadar kudade a asusun banki mallakin mataimakin dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar, Mr Peter Obi, matarsa, iyalansa da na kasuwancinsu, wanda hukumomin gwamnatin Muhammadu Buhari suka dakatar.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Kola Ologbondiyan, daraktan watsa labarai na kungiyar yakin zaben dan takarar shugaban kasa na PDP, wacce aka rabawa manema labarai a ranar Asabar, ta ce tun bayan da aka bayyana Obi a matsayin abokin takarar Atiku yake samun barazana kan hakan.

"Tun bayan zabarsa, Peter Obi, duk da irin yunkurin da jam'iyyar APC take yi na bata sunansa wanda ke zama a banza, yanzu kuma ta ci gaba da yi masa barazana da hanyoyin damfara, da suka hada da yi ma rayuwarsa barazana da ma rayuwar matarsa da 'yayansa.

KARANTA WANNAN: Rahama Sadau ta cika shekaru 25: Kalli sabbin zafafan hotunan da suka rikita maza

Peter Obi

Peter Obi
Source: Depositphotos

"Duba da cewa da yawan 'yan Nigeria na nuna goyon bayansu ga takarar Atiku Abubakar da Peter Obi a matsayin shugaban kasa da mataimakinsa, fadar shugaban kasa Buhari da jam'iyyar APC sun dauki wasu matakan tuggu, da suka hada da kai farmaki ga mutunci da kasuwancin 'yan takara, a yunkurin bata sunansa.

"Fadar shugaban kasa Buhari ta tsorata da irin nasabar Peter Obi, musamman, kwarewarsa a wajen jagoranci, sanin makamar aiki da kuma bin diddigi a aikin gwamnati.

"Idan ba haka ba, me zai sa fadar shugaban kasa ta fara bincike kan Peter Obi, wanda ya bar ofishin gwamnan jihar Anambra shekaru biyar da suka wuce, tare da kyakkyawan sakamako na aiki, martaba da kuma kwarewar aiki, da kuma rashin yarda da cin hanci da rashawa, wanda ya bar kusan N75bn a asusun gwamnatin jihar, ba tare da ana binsa bashi, fansho ko giratuti ba."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.co

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel