Anyi batakashi tsakanin Soji da yan Boko Haram a Jakana, jihar Borno

Anyi batakashi tsakanin Soji da yan Boko Haram a Jakana, jihar Borno

Jami’an rundunar sojin Operation lafiya dole sun samu nasarar fitittikan yan ta’addan a kauyen Jakana da ke karamar hukumar Kaga na jihar Borno.

Kamfanin dillancin labarai ya tattaro cewa yan ta’addan sun kai mumunan hari Jakana ne sa’o’I 12 bayan an fitittikesu a garin Bama da Rann inda suka kona asibiti.

Duk da cewan babu wani jawabi daga bakin hukumar sojin Najeriya har yanzu, rahotanni sun nuna cewa dakarun sunyi musayar wuta da yan ta’addan har suka samu damar kawar da su.

Wani majiya mai karfi cikin jami’an Civillian JTF da akafi sani da kato da gora ya bayyana cewa yan ta’addan sun kawo farmaki ne misalign karfe 8 na daren Juma’a, 7 ga watan Disamba, 2018.

KU KARANTA: Ba dadi: Boko Haram sun sake kai hari Rann, sun kona asibiti daya tilo kurmus

Majiyar ya kara da cewa dakarun soji tare da hadin kan wasu jami’an tsaro sukayi artabu da yan ta’addan wanda aka kwashe akalla awa daya anayi.

Dan bangan ya kare da cewa babu wani jami’in tsaro ko masu farar hula da ya aka rasa ko ya jikkata a wannan hari.

Mun kawo muku rahoton cewa Yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram sun kuma kai mumunan hari Rann, wani gari a karamar hukumar Kala Balge dake jihar Borno. Yan ta'addan sun kona asibitin UNICEF daya tilo dake garin kurmus.

Majiya daga karamar hukumar ya bayyanawa manema labarai cewa jami'an sojin Najeriya sun dakilesu bayan batakashi da sukayi cikin dare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel