2019: Mamba a majalisar wakilai daga arewa ya bawa bawa Buhari gudunmawar motoci 110

2019: Mamba a majalisar wakilai daga arewa ya bawa bawa Buhari gudunmawar motoci 110

A yayin da zaben fitar shekarar 2019 ke kara matsowa, manyan jam'iyyun Najeriya; APC da PDP, na cigaba da zage dantse ta fuskar yakin neman zabe domin ganin sun kai ga samun lashe zabe a kowanne mataki.

Mamba a majiyar wakilai daga jihar Neja bawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, gudunmawar motocin yakin neman zabe guda 110 tare da yin kira ga masu zabe da kada kuri'ar su ga jam'iyyar APC a zabukan shekarar 2019.

Dan majalisar, Umar Bago; mamba a jam'iyyar APC, ya yi wannan bajinta ne a yau, Asabar, a jihar Neja.

Da yake mika gudunmawar motocin ga shugaban jam'iyyar APC a garin Minna, babban birnin Neja, Bago ya bayyana cewar yana da karfin gwuiwar cewar 'yan Najeriya zasu sake zaben shugaba Buhari.

2019: Mamba a majalisar wakilai daga arewa ya bawa bawa Buhari gudunmawar motoci 110

Buhari yayin yakin neman zabe
Source: UGC

Ya bukaci mambobin jam'iyyar APC da su zage dantse tare da yin aiki tukuru domin ganin shugaba Buhari da gwamnan jihar Neja, Abubakar Bello, sun samu nasara a zabe mai zuwa.

A cewar sa, za a raba motocin kamfen din ga shugabannin yakin neman zabe domin su samu saukin shiga kauyuka su wayar da kan jama'a a kan nasarorin da Buhari da gwamna Bello suka samu.

DUBA WANNAN: Da duminsa: Jami'an EFCC sun dira gidan jigo a tafiyar Atiku

Bago ya ce shugaba Buhari ya yi muhimman aiyuka da suka kawo gagarumin canji a rayuwar talakan Najeriya kamar yadda gwamna Bello ya yi a jihar Neja.

A nasa jawabin, mataimakin gwamnan jihar Neja, Alhaji Mohammed Ketsu, ya bukaci mambobin jam'iyyar APC da su alkinta katunan zabensu domin yin amfani da su wajen zaben shugabannin da suke so tare da yin kira ga wadanda suka yi rijista da su gaggauta karbo nasu katunan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel