Ba za mu daina fitowa ba har sai an saki Elzakzaky – Yan shi’a

Ba za mu daina fitowa ba har sai an saki Elzakzaky – Yan shi’a

Mabiya mazhabar Shi’a sun bayyana cewa ba za su daina fitowa zanga-zanga a titunan kasar ba idan har ba’a saki shugabansu, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky wanda ke tsare ba. A ranar Juma'a, 7 ga watan Disamba ne 'yan Shi’an suka yi wani jerin gwano daga babban masallacin juma'ar Abuja.

Kungiyar yan uwa Musulmai yan Shi’a sun bayyana cewa ba za su daina fitowa zanga-zanga a tituna ba idan har ba’a saki shugabansu, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky wanda ke tsare ba.

A ranar Juma'a, 7 ga watan Disamba ne 'yan Shi’an suka yi wani jerin gwano daga babban masallacin juma'ar Abuja inda suka kewaya babban birnin.

Ba za mu daina fitowa ba har sai an saki Elzakzaky – Yan shi’a

Ba za mu daina fitowa ba har sai an saki Elzakzaky – Yan shi’a
Source: Original

Sheikh Abdurrahman Yola wanda daya ne daga cikin jagororin zanga-zangar ya neman a saki Elzakzaky, ya bayyanawa majiyarmu ta BBC Hausa cewa "Shekaru biyu kenan da wata babbar kotu a Abuja ta bayar da iznin sakin shugaban nasu amma gwamnati ta yi burus", inda ya ce sakin shugaban nasu ne kawai mafita.

A watan Disambar 2015 ne dai jami'an tsaron Najeriya suka kama Ibrahim Elzakzaky bayan far wa gidansa bisa zargin tare wa hafsan sojojin kasan kasar hanya a Zariya.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Jami'an EFCC sun dira gidan jigo a tafiyar Atiku

Tun dai wannan lokacin ne 'yan kungiyar ke ta hawa tituna suna zanga-zanga kan kiran a saki shugaban nasu da matarsa da sauran 'yan kungiyar da ke tsare.

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel