Dan majalisar APC ya zargi gwamnatin tarayya da yin karya kan Boko Haram

Dan majalisar APC ya zargi gwamnatin tarayya da yin karya kan Boko Haram

- Dan majalisar tarayya, Sani Mohammed na jam'iyyar APC ya ce ko kadan babu gaskiya cikin ikirarin da gwamnatin Buhari tayi na cewa soji sun ci galaba kan Boko Haram

- Dan majalisar ya yi wannan jawabin ne bayan shi da tawagarsa sun kai ziyara wasu garuruwa a yankin Arewa maso gabas domin duba halin da ake ciki

- Mohammed ya ce har yanzu mutanen Arewa maso gabas suna cikin bala'i kuma karya ce kawai gwamnati keyi na cewa an samar da tsaro a yankin

Hon. Sani Mohammad, ciyaman din kwamitin majalisar wakilai kan ayyukan taimakawa ya ce ikirarin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tayi na cewa ta an samu zaman lafiya a yankin Arewa maso gabashin kasar karya ne.

Dan majalisar wadda dan jam'iyyar APC ne ya ce yankin na cikin bala'i kuma ya bayyana fargabarsa kan yiwuwar fitinar ta yadu zuwa sauran sassan Najeriya kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Dan majalisar APC ya zargi gwamnatin tarayya da yin karya kan Boko Haram

Dan majalisar APC ya zargi gwamnatin tarayya da yin karya kan Boko Haram
Source: UGC

Mr Mohammed ya yi wannan furucin ne a yayin da ya ke yiwa takwarorinsa bayani bayan ziyarar da ya kai a wasu sassan yankin. Oak Tv ta wallafa faifan bidiyon jawabin da ya yi.

DUBA WANNAN: 2019: Atiku ya fadi abinda gwamnatinsa ba za ta yarda da shi ba idan aka zabe shi

"kwanan nan muka dawo daga ran gadi a jihohin Borno da Yobe kuma abinda muka gano shine yankin na cikin bala'i kamar yadda Hon. Chika ya ce," dan majalisar ya ce gaskiyar lamarin shine har yanzu yankin na fuskantar babban barazana daga kungiyar Boko Haram.

"A ranar Alhamis da muka je Maiduguri, mayakan Boko Haram sun kai hari a sansanin 'yan gudun hijira da ke Dalori 2 wadda ke kallon Jami'ar Maiduguri. Sun kone sassa da dama na sansanin, sun kashe mutane 8 kuma sun sace mata sun tafi da su daji ba tare wani ya kallubalance su ba."

Bisa ga dukkan alamu, kalaman da gwamnati tayi na cewa an samar da zaman lafiya a yankin ba komai bane illa tsabar karya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha fadi cewa sojin Najeriya sun ci galaba a kan mayakan Boko Haram kuma sun karya lagwan su har ma a jawabinsa na ranar sabuwar shekarar 2018 ya ce sojojin sun dade da cin galaba a kan Boko Haram.

Sai dai a cikin 'yan kwanakin nan, mayakan na Boko Haram na tsananta kai hare-hare sansanin sojin Najeriya inda suka kashe soji sama da 100.

"Mutanen da ke Bama ba su wuce 200 ba yanzu. Maganar cewa an samu zaman lafiya ko abubuwan sun daidaita a yankin Arewa maso gabas ba gaskiya bane. Karya ce," inji dan majalisar.

Mr Mohammed ya ce shi da tawagarsa sun gaza zuwa Chibok saboda babu tsaro a garin amma sun tafi Bama da Gashua.

"Kai ziyara zuwa Chibok yana cikin aikin mu. Amma Chibok baya shiguwa. Kwanaki uku da suka shude, Boko Haram sun kai farmaki kauyen su shugaban hafsin hafsoshin Najeriya suka kashe mutane kuma su kayi tafiyarsu ba tare da wani ya tanka musu ba. Maganar gaskiya itace wasu garuruwan na karkashin ikon 'yan ta'ada ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel