Gwamnatin jihar Bayelsa ta sha alwashin hukunta wadanda suka haddasa tarzoma a Zaben 2015

Gwamnatin jihar Bayelsa ta sha alwashin hukunta wadanda suka haddasa tarzoma a Zaben 2015

- Gwamnatin jihar Bayelsa ta ce ba bu ga wadanda suka haddasa tarzoma cikin jihar a zaben 2015

- Majalisar zantarwa ta jihar Bayelsa ta sha alwashin wadanda ke da hannu cikin muguwar ta'adda ta tashin-tashina a zaben gwamnan jihar da gudana a shekarar 2015

- Gwamnatin jihar ta yanke shawarar hukunta wadanda suka haddasa tarzoma a zaben 2015 bayan hukumae Shari'a ta jihar ta kammala binciken ta

Mun samu rahoton cewa, gwamnatin jihar Bayelsa karkashin jagorancin gwamna Seriake Dickson, ta sha alwashin hukunta wadanda suka haddasa tarzoma yayin babban zaben kasa da ya gudana a shekarar 2015 da ta gabata.

Gwamnatin a jiya Juma'a yayin gudanar da zaman majalisar zantarwa na jihar, ta sha alwashin hukunta dukkanin masu hannu cikin aikata muguwar ta'ada wajen haddasa tarzoma da ta auku a jihar yayin zaben 2015.

Majalisar yayin zamanta na 100 da ta gudanar bisa jagorancin gwamna Dickson, ta yanke wannan hukunci bayan da cibiyar Shari'a ta jihar ta gabatar da sakamakon binciken da ta aiwatar kan babban zaben da ya gudana kimanin shekaru hudu da suka gabata.

Gwamnan jihar Bayelsa; Seriake Dickson

Gwamnan jihar Bayelsa; Seriake Dickson
Source: Depositphotos

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, majalisar ta bayyana cewa, ba bu afuwa ko rangwami ga wadanda suka haddasa mummunar ta'ada ta tarzoma cikin jihar, inda a halin ta fantsama cikin shawarwari na hukunci da za ta zartar a kansu.

A yayin ganawarsa da manema labarai, sakataren gwamnatin jihar Mista Kemela Okara, ya bayyana cewa hukuncin da majalisar zantarwa ta jihar ta yanke na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da yiwa doka da'a da kuma kiyayewa.

KARANTA KUMA: Hukumar EFCC na taimakon 'Yan Siyasa wajen cimma manufa - ZUF

Majiyar jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, wannan lamari na hukunta wadanda suka haddasa tarzoma a zaben 2015 zai kasance izina yayin da babban zabe na 2019 ke ci gaba da gabatowa domin Hausawa na cewa akan tauna tsakuwa domin aya ta ji tsoro.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, jam'iyyar adawa ta PDP, ta yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari raddi dangane da rashin amincewarsa da dokar gyara salon zabubbukan kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel