Zargin Tuggu: Hukumar EFCC na taimakon 'Yan Siyasa wajen cimma manufa a jihar Zamfara - ZUF

Zargin Tuggu: Hukumar EFCC na taimakon 'Yan Siyasa wajen cimma manufa a jihar Zamfara - ZUF

- Kungiyar Zamfara Unity Forum na zargin hukumar EFCC da kulla makircin siyasa a jam'iyyar APC reshen jihar

- Har yanzu Hukumar INEC ba ta amince da zabukan fidda gwanayen takara na jam'iyyar APC

- An kirayi shugaban kasa Buhari ya yiwa EFCC kashedi kan shiga lamarin siyasar APC a Zamfara

Wata kungiyar hadin kai ta yi zargin cewa, hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC, na da hannu dumu-dumu cikin kulle-kullen tuggu da wasu 'yan siyasa domin kawo rudani yayin zaben gwamnan jihar Zamfara a babban zabe na 2019.

Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya ruwaito, kungiyar na zargin cewa wasu 'yan siyasa na ribatar hukumar EFCC wajen kulla kitumurmurar kawo rudani da cimma manufofinsu dangane da zaben kujerar gwamna a jihar Zamfara.

Kungiyar ta Zamfara Unity Forum, ZUF, ta bayyana cewa, kulle-kullen tuggu da kitimurmura ya sanya hukumar EFCC ta tsare dan takarar kujerar gwamnan jihar Zamfara na jam'iyyar APC, Dauda Lawal, har na tsawon mako guda.

Hukumar EFCC na taimakon 'Yan Siyasa wajen cimma manufa - ZUF

Hukumar EFCC na taimakon 'Yan Siyasa wajen cimma manufa - ZUF
Source: Depositphotos

Kawowa yanzu dai rahotanni sun bayyana cewa, gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Abubakar Yari, yayin da ya ke ci gaba da kai ruwa rana wajen tsayar da kwamishinan kudi na jiharsa, Mukhtar Idris, a matsayin dan takarar gwamna na jam'iyyar APC hakarsa ba ta cimma ruwa ba.

Majiyar jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, kungiyar ZUF ta yi zargin cewa, gwamna Yari tare da hadin gwiwar hukumar EFCC sun dukufa wajen sauya tsayayyen dan takarar gwamnan jihar Zamfara na jam'iyyar APC.

KARANTA KUMA: 2019: Za a dauki kwanaki 5 kafin bayyana sakamakon zaben shugaban kasa - Bincike

Har ila yau, hukumar zabe ta kasa watau INEC, na ci gaba da kasancewa akan bakanta na rashin amincewa da duk wasu 'yan takara na jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara sakamakon yiwa dokarta karan tsaye yayin gudanar da zabukanta na fidda gwanayen takara.

Kungiyar ta kuma kirayi shugaban kasa Buhari akan gaggauta yiwa hukumar EFCC kashedi dangane da wannan lamari, inda ta ce hakan na iya janyo rashin aminci a zukatan al'ummar kasar nan dangane da ingancin zaben 2019.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel