2019: Za a dauki kwanaki 5 kafin bayyana sakamakon zaben shugaban kasa - Bincike

2019: Za a dauki kwanaki 5 kafin bayyana sakamakon zaben shugaban kasa - Bincike

- Zaben shugaban kasa na 2019 za ya dauki kwanaki 5 kafin bayyanar sakamakon sa

- Jam'iyyu 73 ne za su fafata yayin babban zaben kasa na 2019

- Mutane kimanin Miliyan 83 za su jefa kuri'un su a zaben 2019

Binciken manema labarai na jaridar The Punch a yau Asabar ya bayyana cewa, zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu na shekarar 2019, za ya dauki kwanaki biyar kafin a bayyana sakamakon sa.

Rahotanni da dama da suka samo tushe daga hukumar zabe ta kasa watau INEC sun bayyana cewa, akwai yiwuwar sakamakon zaben 2019 ba za ya bayyana ba har sai bayan kwanaki biyar a sanadiyar yawaitar jam'iyyun takara.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wannan jinkiri na bayyana sakamakon zaben shugaban kasa da za a gudana a badi za ya bayu ne a sakamakon yawan adadi na kimanin jam'iyyu 73 da za su fafata da kuma adadin wadanda za su kada kuri'u da a halin yanzu hukumar INEC ta yiwa mutane 84m rajistar zabe.

2019: Za a dauki kwanaki 5 kafin bayyana sakamakon zaben shugaban kasa - Bincike

2019: Za a dauki kwanaki 5 kafin bayyana sakamakon zaben shugaban kasa - Bincike
Source: Depositphotos

Tarihi ya tabbatar da cewa, jam'iyyar PDP da kuma AD su kadai ne jam'iyyu biyu kacal da suka fafata takarar kujerar shugaban kasa yayin zaben kasa da aka gudanar a ranar 27 ga watan Fabrairu na shekarar 1999, inda sakamakon zaben ya bayyana a ranar 1 ga watan Maris, kwanaki biyu kenan bayan gudanar sa.

A shekarar 2003 kuma, jam'iyyu 20 sun yi gumurzu yayin zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 19 ga watan Afrilu, inda bayan kwanaki uku sakamakon sa ya bayyana a ranar 22 ga watan na Afrilu.

Zaben shugaban kasa da ya gudana a ranar 21 ga watan Afrilu na shekarar 2007 tsakanin jam'iyyu 18, sakamakon sa kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito ya bayyana bayan kwanaki biyu kacal da gudanarsa da hakan ya yi daidai da ranar 23 na watan Afrilu.

Jam'iyyu 20 sun gwabza da juna yayin zaben shugaban kasa na 2011 da aka gudanar a ranar 16 ga watan Afrilu, da ko shakka ba bu sakamakon sa ya bayyana kwanaki biyu bayan gudanarsa a ranar a ranar 18 na wannan wata.

Kazalika zaben 2015 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zamto zakara ya gudana a tsakanin jam'iyyu 14 da aka gudanar a ranar 28 da kuma 29 ga watan Maris na wannan shekara. An bayyana sakamakon sa a ranar 1 ga watan Afrilu kwanaki biyu kenan bayan gudanarsa.

KARANTA KUMA: Tura ta kai Bango - PDP ga shugaban Kasa Buhari

Sai dai wani babban jami'in hukumar zabe ta kasa da ya bukaci a sakaya sunansa yayin ganawa da manema labarai ya bayyana cewa, akwai yiwuwar sakamakon zaben 2019 zai bayyana bayan kwanaki biyar da gudanarsa cikin fiye da rumfunan zaben 120, 000 da ke fadin kasar nan.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta dukufa wajen tabbatar da hadin kai a kasar nan yayin da cimma nasara a zabe na watan jibi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel