2019: Atiku ya fadi abinda gwamnatinsa ba za ta yarda da shi ba idan aka zabe shi

2019: Atiku ya fadi abinda gwamnatinsa ba za ta yarda da shi ba idan aka zabe shi

Dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya yi alkawarin cewa ba zai bari wasu tsiraru su rika juya gwamnatinsa ba bayan ya yi nasara, hakan yasa ya yi alkawarin zai kafa gwamnatin hadaka da sauran jam'iyyun da suka goyi bayansa.

Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugabancin kasa karkashin inuwar jam'iyyar PDP ya ce zai kafa gwamnatin hadaka bayan ya lashe zaben 2019 kuma ba zai amince wasu tsirarun azzalumai su rika juya akalar gwamnatinsa ba.

Ayiku ya yi wannan jawabin ne a ranar Juma'a a Abuja yayin da ya ke ganawa da hadakan jam'iyyun siyasan Najeriya CUPP da ke dauke da jam'iyyun siyasa 45 da suka goyi bayansa a matsayin dan takarar shugabancin kasarsu.

2019: Atiku ya fadi abinda gwamnatinsa ba za ta yarda da shi ba idan aka zabe shi

2019: Atiku ya fadi abinda gwamnatinsa ba za ta yarda da shi ba idan aka zabe shi
Source: Facebook

DUBA WANNAN: 2019: Ba za ayi adalci ba muddin Buhari bai amince da gyaran dokar zabe ba - SDP

Ya ce Najeriya na fuskantar kallubalen tsaro, tabarbarewar tattalin arziki da wasu matsalalolin.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriyan ya ce ya shiga wannan takarar ne domin ya kawar da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki wadda ya ce ta gaza cikawa al'umma alkawuran da ta dauka yayin kamfen.

"Idan da bamu kori sojoji ba, da yanzu ba mu batun demokuradiya ko jam'iyyun siyasa. Saboda haka akwai babban aiki a gabanmu. Ba zaku koma ku zauna ba kawai bayan kun ce kuna goyon bayan takara ta. Ina son in tabbatar muku da cewa zamu kafa gwamnatin hadaka saboda haka babu wasu tsiraru da za su rika juya gwamnati," inji Atiku.

Tsohon Ministan harkokin kasashen waje kuma jigo cikin hadakar jam'iyyun siyasan adawa ta CUPP, Cif Tom Ikimi ya ankarar da mahalarta taron cewa jam'iyyar APC tana kokarin shiga cikin CUPP domin ta kawo rudanni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel