Tura ta kai Bango - PDP ga shugaban Kasa Buhari

Tura ta kai Bango - PDP ga shugaban Kasa Buhari

- Rashin amincewar shugaban kasa Buhari da sabuwar dokar gyaran zabe ta fusata jam'iyyar PDP

- Shugaba Buhari ya ce ba zai amince da gyara dokar zabe ba sai bayan zaben 2019

- PDP ta ce fargabar shan kasa a zaben 2019 ta sanya shugaba Buhari ya ki amincewa da gyara dokar zabe

A jiya Juma'a cikin garin Abuja, shugaban kasa Muhammadu Buhari, karo na hudu kenan, ya sake watsi da dokar gyara zaben kasar nan da tuni majalisar dattawa da kuma majalisar wakilai suka bayyana sahalewarsu da ita.

Shugaban kasa Buhari cikin rubutacciyar wasikarsa da ya aike da ita zuwa ga majalisar dokokin tarayyar kasar nan, ya bayyana dalilansa kan cewa ba bu dace ya amince da wannan sabuwar doka a daidai wannan lokaci da zaben 2019 ke bakin gaba.

Kamar yadda shafin jaridar Vanguard ta ruwaito, shugaba Buhari ya bayyana cewa samun amincewarsa kan wannan doka ba za ta tabbata ba sai bayan zaben 2019 domin fargabarsa akan aiwatar da hakan ka iya jefa kasar nan cikin rudani.

Tura ta kai Bango - PDP ga shugaban Kasa Buhari

Tura ta kai Bango - PDP ga shugaban Kasa Buhari
Source: UGC

A sanadiyar haka kungiyar yakin neman zabe ta jam'iyyar PDP, ta kirayi majalisar dokokin tarayyar kasar nan kan gaggauta yin gaban kanta na kaddamar da sabuwar doka ta gyara salon zabe ba tare da amincewar jagoran kasar nan ba.

A yayin mayar da martani dangane da wannan lamari na gyaran zabe, jam'iyyar PDP cikin wata sanarwa da sanadin kakakin ta, Mista Kola Ologbondiya ta bayyana cewa, hukuncin shugaba Buhari wata kitimurmura ce ta toshe magudanai na kwaranyawa kasar nan romon dimokuradiyya.

Sai dai ko shakka shugaba Buhari cikin rubutacciyar wasika ya aike da ita a ranar 6 ga watan Dasumba, ya bayar da tabbacinsa ga jagororin majalisar tarayya kan amincewa da sabuwar dokar ta gyara salon zaben kasar nan bayan an kammala babban zaben kasa na badi.

KARANTA KUMA: Ba bu PDP ba bu cin Zabe a jihar Akwa Ibom - Dan Takarar Gwamna na jam'iyyar APC

Mista Kola ya kara da cewa, rashin amincewar Buhari kan sabuwar dokar gyaran zabe wata manuniya ce da ke haskaka fargabar sa ta bankado tuggun da jam'iyyar APC ta dukufa wajen kullawa domin cimma nasara a zaben 2019.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugabancin jam'iyyar APC ta bayyana cewa amincewar shugaban Buhari kadai take tsumayi domin daukar matakai kan gwamna jihar Imo, Rochas Okorocha da kuma takwaransa na jihar Osun, Ibikunle Amosun.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel