Zaben 2019: Atiku, Obi, da shuwagabannin PDP sun yi wata ganawa a Fatakwal

Zaben 2019: Atiku, Obi, da shuwagabannin PDP sun yi wata ganawa a Fatakwal

- Shuwagabannin PDP sun yi wata ganawa a Fatakwal, jihar River, don tattauna wasu muhimman batutuwa da suka shafi zaben 2019 da ke gabatowa

- Kafin gudanar da taron, Mr Wike ya fara jan jawagar kungiyar yakin zaben dan takarar shugaban kasar PDP zuwa rangadi a ofishin yakin zaben PDP reshen jihar Rivers

- Daga cikin mahalarta taron akwai Atiku Abubakar; Mr Obi; Mr Secondus; Mr Wike; Mr Okowa; Mr Ayade; Mr Saraki; Mr Dogara; Mr Tambuwal; Mr Umahi; da Ben Bruce da sauran su

A ranar Juma'a, 8 ga watan Disamba, 2018 shuwagabannin jam'iyyar PDP suka yi wata ganawa a ofishin yakin zaben jam'iyyar da ke Fatakwal, jihar River, don tattauna wasu muhimman batutuwa da suka shafi zaben 2019 da ke gabatowa.

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar, Atiku Abubakar, abokin takararsa, Peter Obi, Darakta Janar na kungiyar yakin zaben dan takarar shugaban kasar, Bukola Saraki, da mataimakin shugaban majalisar dattijai, Ike Ekweremadu, na daga cikin wadanda suka halarci taron.

Haka zalika, kakakin majalisar wakilan tarayya, Yakubu Dogara tare da Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers na daga cikin mahalarta wannan taro.

KARANTA WANNAN: 2019: PDP ta yi watsi da Kashamu, ta mika tuta ga 'yan takarar gwamnonin jihohi 3

Zaben 2019: Atiku, Obi, da shuwagabannin PDP sun yi wata ganawa a Fatakwal

Zaben 2019: Atiku, Obi, da shuwagabannin PDP sun yi wata ganawa a Fatakwal
Source: Twitter

Shugaban jam'iyyar na kasa, Uche Secondus; Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto; Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta; Gwamna Dave Umahi na Ebonyi; da kuma takwaransa na jihar Cross River, Ben Ayade na daga cikin wadanda suka halarci taron.

Kafin gudanar da taron, Mr Wike ya fara jan jawagar kungiyar yakin zaben dan takarar shugaban kasar PDP zuwa rangadi a ofishin yakin zaben PDP reshen jihar Rivers don ganin yadda tsarinsa yake.

DUBA WANNAN: Sakamakon fasa kwabri: Kotun Nigeria ta garkame wani dan kasar Congo shekaru 4 a gidan kaso

Haka zalika Mr Wike ya fara marabtar bakin tare da gudanar da wani taron ganawa na shuwagabannin jam'iyyar PDP a gidan gwamnatin jihar, gabanin babban taron nasu.

Daga cikin wadanda suka halarci taron a gidan gwamnatin jihar akwai Atiku Abubakar; Mr Obi; Mr Secondus; Mr Wike; Mr Okowa; Mr Ayade; Mr Saraki; Mr Dogara; Mr Tambuwal; Mr Umahi; da Ben Bruce.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.co

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel