Yajin aikin ASUU: Malamin jami'ar Anambra ya yi shigar 'Superman' don koyar da dalibai

Yajin aikin ASUU: Malamin jami'ar Anambra ya yi shigar 'Superman' don koyar da dalibai

- Wani malamin jami'ar jihar Anambra, ya sanya kayan 'Spiderman' don koyar da dalibai, a yayin da kungiyar ASUU ke ci gaba da yajin aiki a jami'o'i dake fadin kasar

- A lokacin da malamin ya shiga ajin, yaki waiwayar daliban da ke ambaton sunansa na gaskiya, inda yake ci gaba da daukar kansa a matsayin 'Spiderman'

- A kwanakin baya ya shaidawa daliban cewar, wanda duk ke son tattaunawar karshe da shi gabanin fara kare project dinsu, to ya tsumayi zuwan 'Spiderman' don taimaka masa

Wani labari da Legit.ng Hausa ta ciki karo da shi a shafin jaridar Punch, na nuni da cewa, wani malamin jami'ar jihar Anambra, wacce aka fi sani da jami'ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu, ya sanya kayan 'Spiderman' don koyar da dalibai, a yayin da kungiyar ASUU ke ci gaba da yajin aiki a jami'o'i dake fadin kasar.

Malamin wanda aka dauki hotonsa sanye da kayan, a lokacin da yake fitowa daga cikin motarsa zuwa ajin da zai koyar a ranar Laraba, 5 ga watan Disamba, 2018, yayi hakanne don koyar da daliban sa da ke karatu a matakin 'Postgraduate.'

KARANTA WANNAN: APC za ta dauki kwakkwaran mataki kan Amosun da Okorocha da zaran Buhari ya amince

Yajin aikin ASUU: Malamin jami'ar Anambra ya yi shigar 'Superman' don koyar da dalibai

Yajin aikin ASUU: Malamin jami'ar Anambra ya yi shigar 'Superman' don koyar da dalibai
Source: Facebook

Rahotanni sun bayyana cewa a lokacin da malamin ya shiga ajin, yaki waiwayar daliban da ke ambaton sunansa na gaskiya, inda yake ci gaba da daukar kansa a matsayin 'Spiderman' da ya zo koyar da karatu.

A cewar pulse.n, a baya ya shaidawa daliban cewar, wanda duk ke son tattaunawar karshe da shi gabanin fara kare kundin nazari da bincikensu na kammala karatu (project), to ya tsumayi zuwan 'Spiderman' don taimaka masa akan shirye shiryen karshe.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.co

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel