2019: Ba za ayi adalci ba muddin Buhari bai amince da gyaran dokar zabe ba - SDP

2019: Ba za ayi adalci ba muddin Buhari bai amince da gyaran dokar zabe ba - SDP

- Shehu Gabam, sakataren jam'iyyar SDP na kasa ya ce rashin saka hannu kan kudirin zabe da shugaban kasa bai yi ba ya nuna ba za ayi a adalci a 2019

- Gabam ya ce akwai baraka sosai a harkar zaben Najeriya kuma yiwa dokar zaben garambawul ne kawai zai magance hakan

- Gaban ya bayyana cewa hukumar zabe mai zaman kanta INEC da hukumomin tsaro suma suna taka rawa wajen kawo cikas a zaben

Shehu Gabam, sakataren jam'iyyar SDP na kasa kuma abokin dan takarar dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar ya ce bai tsamanin za a iya gudanar da sahihiyar zabe a 2019 ba saboda rashin amincewa da kudirin yiwa dokar zabe garambawul da shugaba Buhari bai yi ba.

Ya ce 'yan siyasa sun dauke zabe abin a mutu ko ayi rai a madadin kafar yiwa kasa hidima kana hukumar INEC da hukumomin tsaro suma duk suna taka rawa wajen tabarbarewar lamuran kuma za a iya kawo gyaran ne bayan amincewa da kudirin yiwa dokar zaben garambawul kamar yadda Tribune ta ruwaito.

2019: Ba za ayi adalci ba muddin Buhari bai amince da gyaran dokar zabe ba - SDP

2019: Ba za ayi adalci ba muddin Buhari bai amince da gyaran dokar zabe ba - SDP
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Atiku ya fadi siffar irin gwamnatin da yake fatan kafa wa

A hirar da ya yi da Ishola Michael, Gabam ya ce, "Babu yadda za a iya gudanar da sahihiyar zabe idan 'yan siyasa sun mayar da zabe abin a mutu ko ayi rai a madadin hanyar yiwa kasa hidima. Galibi 'yan siyasa sukan kawo cikas domin su samu nasara a zabe.

"Ba INEC na kadai matsalar ba, yan siyasa suna daga cikin wadanda ke janyo matsaloli a harkokin zabe amma shugaban kasa yaki amincewa da kudirin yiwa dokar zabe garambawul, wannan zai bawa 'yan siyasa damar suyi dukkan abubuwan da suka ga dama.

"Duk dan siyasan da zai iya tattaro 'yan daba shine zai tafiyar da abubuwan da za su faru a rumfar zabe kamar dangwale ba bisa ka'ida ba da sace akwatin zabe, abubuwan suna da yawa. Daga lokacin da muka sanya kasa a gaba, za mu fara kirkiro dokokin da za su dabbaka demokradiyya da dawo da doka da oda da kuma adalci."

A wani rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa kungiyar Yarabawa ta Afenifere ta bayyana cewa ba tayi imani INEC za ta gudanar da sahihiyar zabe ba a 2019 saboda shugaba Muhammadu Buhari na ya nada shugaban hukumar saboda akwai yiwuwar zai nuna fifiko ga wanda ya nada shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel