Buhari ya yi sabbin nade-nade a CBN, NNPC da NPA

Buhari ya yi sabbin nade-nade a CBN, NNPC da NPA

Domin inganta tsimi da tanadi da kuma dakile zurarewar kudi daga aljihun gwamnati, musamman a hukumomin tattara kudaden haraji na gwamnatin tarayya, shugaba Buhari ya amince da nadin wasu ma'aji-ma'aji a matsayin darektoci masu kula da adani a wasu hukumomi da ma'aikatun gwamnatin tarayya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da yin canjin wuraren aiki ga ma'aji-ma'aji a hukumomin dake sanarwa gwamnati kudaden shiga da wasu ma'aikatun gwamnati. Ma'aji-ma'ajin zasu yi aiki a matsayin darektocin ajiya a sabbin wuraren aikinsu.

Babban akawu na kasa (AGF), Ahmed Idris, ne ya sanar da hakan yayin karbar bakuncin shugaban kasa da jami'an cibiyar bawa akawu horon kwarewa a aiki (ICAN) yayin wata ziyarar aiki da suka kai ofishinsa.

A cewar Idris, an yi sabbin nade-naden ne domin inganta tsimi da tanadi a hukumomin gwamnati dake tattara kudaden shiga.

Buhari ya yi sabbin nade-nade a CBN, NNPC da NPA

Buhari ya yi sabbin nade-nade a CBN, NNPC da NPA
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Buhari sai ya fadi, in ji Atiku

Hukumomin da abin ya shafa sun hada da: hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta kasa (NPA), hukumar kula da jigila ta cikin ruwa (NIMASA), babban bankin kasa (CBN), kamfanin dillancin man fetur na kasa NNPC), hukumar kula da aiyukan kwastam (NCS), hukumar kula da harkokin sadarwa (NCC), da hukumar tattara haraji ta kasa (FIRS) da sauransu.

Idris ya kara da cewa daga cikin aiyukan sabbin darektocin akwai kawo sabbin canje-canje a bangaren adana kudaden shigowa bisa tsarin gwamnati na bunkasa hanyoyin shiga da tara kudade.

"Gwamnati ta damu da yadda kudade ke zurarewa a hukumomin tattara kudaden haraji, a saboda haka ne muka tura kwararru da zasu yi amfani da ilimin fasahar zamani domin gano wa tare da dakile zurarewar kudi daga aljihun gwamnati," a kalaman Idris.

Kazalika ya bayyana cewar kwazo ne zai zama ma'aunin dadewar sabbin darektocin a duk inda aka tura su aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel