Kukan kurciya: Abdulsalami ya ceba zai iya zama shugaban Nigeria yana da shekaru 77 ba

Kukan kurciya: Abdulsalami ya ceba zai iya zama shugaban Nigeria yana da shekaru 77 ba

- Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce ba zai iya dawowa ya shugabanci Nigeria a mulkin farar hula yana da shekaru 77 ba

- Ya ce lokaci yayi da ya kamata wadanda suka tsufa su koma daga gefe suna kwaba tare da karfafa guiwar matasan kasar dangane da shugabancin kasar

- Dangane da zaben 2019 da ke gabatowa, Abdulsalami, ya bukaci daukacin jama'a da su sanya zaman lafiyar kasar a zukatansu

Tsohon shugaban kasar Nigeria a mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce ba zai iya dawowa ya shugabanci Nigeria a mulkin farar hula ba, bayan da aka tambaye shi irin abubuwan da zai yi idan aka zabe shi yana da shekaru 77.

Ya ce lokaci yayi da ya kamata wadanda suka tsufa su koma daga gefe suna kwaba tare da karfafa guiwar matasan kasar dangane da shugabancin kasar.

Ya bayyana hakan a ranar Alhamis a bukin kaddamar da wani littafi kan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Patrick Yakowa, a lokacin da mai tsara jawabai a taron, Abba Zayyan Abba, yayi addu'ar Allah ya sa Abdulsalam ya zama shugaban kasar Nigeria a mulkin farar hula.

KARANTA WANNAN: Yadda sakacin gwamnatin APC da Buhari ya jawo asarar sama da ayyuka 12m - Atiku

Kukakn kurciya: Abdulsalami ya ceba zai iya zama shugaban Nigeria yana da shekaru 77 ba
Kukakn kurciya: Abdulsalami ya ceba zai iya zama shugaban Nigeria yana da shekaru 77 ba
Asali: Depositphotos

Abdulsalami ya mayar masa da jawabi kan cewa: "A jawabin bude taron, Abba, ka yi wata addu'a, sai dai ko a lokacin ina girgiza kaina ne daga hagu zuwa dama. Daya daga cikin musabbabin rayuwa shine sanya matasa kan turba ta siyasa don basu damar nuna tasu banjintar, na daga cikin dalilin amincewa da dokar "Not Too Young to Run" don baiwa matasa damar tsayawa takara, saboda idan na zama shugaban kasa ina da shekaru 77 me zan tabuka? Ba na ma iya tafiya da kyau. Na gode maka da addu'arka kuma ina fatan matasanmu zasu ci gaba da shugabantarmu."

Dangane da zaben 2019 da ke gabatowa, Abdulsalami, wanda shine shugaban hukumar zaman lafiya ta kasa, ya bukaci daukacin jama'a da su sanya zaman lafiyar kasar a zukatansu da kuma kauracewa yakin zaben da zai haddasa rikicin addini ko na kabilanci.

Ya ce Yakowa ya samar da nagartacciyar taswira da gano ma'adanan kasa da Allah ya sanya a cikin Nigeria.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.co

Asali: Legit.ng

Online view pixel