2019: Ba muyi imani da INEC ba - Afenifere

2019: Ba muyi imani da INEC ba - Afenifere

Kungiyar Yarabawa ta Afenifere ta bayyana damuwan ta a kan hukumar zabe INEC inda ta ce zai yi wuya tayi adalci a zaben 2019 saboda shugaba Buhari ne ya nada shugaban hukumar. Tayi kira da cewa ayi garambawul a hukumar muddin ana son zabe na adalci.

Kungiyar al'ummar Yarabawa ta Afenifere ta ce ba ta gamsu da irin shirin da hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta yi ba game da zaben 2019 inda ta ce da wuya za ta iya gudanar da sahihiyar zabe.

Daya daga cikin shugabanin kungiyar, Ayo Adebanjo ne ya furta hakan yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Toru-Orua, kauyen su Gwamna Seriake Dickson na jihar Bayelsa yayin jana'izar mahifiyarsa Mrs Goldcoast Dickson.

Mr Adebanjo ya yi kira da cewa a canja shugaban INEC domin a cewarsa babu yadda za ayi shugaban hukumar zaben ya yi adalci a zabe tsakanin wanda ya nada shi da wani daban kuma akwai yiwuwar hakan ta faru a 2019.

2019: Ba muyi imani da INEC ba - Afenifere

2019: Ba muyi imani da INEC ba - Afenifere
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Buhari sai ya fadi, in ji Atiku

A cewarsa, "Kamar yadda muka fadi a baya, ba mu amince da INEC ba a yadda ta ke yanzu. Hasali ma, muna son a sake ma'aikatan hukumar baki daya. A ganin mu, idan ana son sahihiyar zabe, bai kamata a samu wani alaka tsakanin shugaban INEC da shugaban kasa ba."

Wani sako mai dauke da saka hannun mai bawa gwamnan Bayelsa shawara a fanin yada labarai, Fedelis Soriwei ya ce shugaban na Afenifere ya kuma ce har yanzu kungiyar tana kan bakan ta na neman a sauya tsarin rabon arzikin kasa.

Mr Adebanjo ya yi kira da 'yan Najeriya su zabi dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP a 2019, Atiku Abubakar saboda shine sai hada kan al'ummar kasar waje guda kuma ya kawo cigaba da walwala.

A yayin da yake mika ta'aziyyarsa ga iyalan Dickson, ya ce Madam Goldcoast albarka ce ga Najeriya saboda yadda tayi tarbiyar da kamar gwamna Dickson wanda ya nuna cewa shi shugaba na nagari. Ya kuma yi addu'a Allah ya jikanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel